Ana Dakon Hukuncin Kotu, Aminu Ado Ya Magantu kan Mulkin Tinubu, Nadin Ganduje
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa kafa hukumar raya kiwo da makiyaya ta kasa
- Basaraken ya ce wannan mataki zai kawo ci gaba da zaman lafiya a Arewacin Najeriya da ma sauran yankuna
- Sarkin ya jinjinawa Farfesa Attahiru Jega da Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin jagorantar kwamitin hukumar
- Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci shugabannin Fulani su jajirce wajen inganta taron kasa da ilimantar da jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano na 15, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu a Najeriya.
Basaraken ya yaba wa Shugaban kasa, Bola Tinubu bisa kafa hukumar raya kiwo da makiyaya ta kasa.

Asali: Facebook
Aminu Ado ya kwarara yabo ga Bola Tinubu
Jawabin Sarkin ya fito ne ta bakin mai magana da yawun fadarsa, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, wanda ya fitar da sanarwa da Punch ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya ce hakan wani shiri ne a matsayin “mataki mai tarihi da jarumta” wanda zai sauya rayuwar makiyaya Fulani tare da tabbatar da zaman lafiya a Arewa.
A cewar sanarwar:
“Wannan shiri da Shugaba Tinubu ya dauko lokaci ne da ya dace kuma yana da girma matuka.
“Wannan alama ce ta jajircewar gwamnati wajen magance matsalolin da ke damun makiyaya da kuma samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.”
Sarkin ya yi maraba da nadin kwamitin da zai jagoranci aiwatar da shirin, wanda Farfesa Attahiru Jega da Dr. Abdullahi Ganduje ke jagoranta.
Ya ce:
“Idan da irin su Farfesa Jega da Ganduje za su jagoranci wannan aiki, muna da kwarin gwiwa cewa za a samu nasara."

Asali: UGC
Aminu Ado ya shawarci Fulani a Najeriya
Basaraken ya bukaci shugabannin kungiyar Fulani su dage don ganin taron kasa na makiyaya mai zuwa ya zama nasara, tare da hada kan jama’a.
Sarkin ya yaba da kokarin kungiyar Fulani wajen yayata ilimi a cikin al’umma, ya ce hakan ne zai kawo ci gaba da wayewar kai.
A baya, shugaban kungiyar Fulani, Alhaji M.B. Lamido ya kai wa Sarkin ziyarar girmamawa da ta’aziyya dangane da kashe wasu mafarauta daga Kano a Edo.
Lamido ya bayyana bakin ciki game da kisan, yana addu’a ga Allah ya jikansu, ya kuma ba iyalansu hakurin jure rashin.
Ya kuma yi bayani kan taron kasa da kungiyar Fulani ke shirin gudanarwa, inda ya nemi goyon bayan masarautar Kano.
A cewarsa:
“Muna fatan hada kan Fulani da wayar da su ta hanyar ilimin addini da na zamani, da kuma horas da su kan sana’o’i."
Rikicin sarauta a Arewacin Najeriya
A cikin ‘yan shekarun nan, arewacin Najeriya na fama da rikice-rikice na sarauta, inda ake ci gaba da ganin sauke sarakuna daga masarautu daban-daban.
Saukewar da ta fi daukar hankali ita ce na tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sauke a shekarar 2020 bisa zargin rashin biyayya da wuce iyaka a magana kan lamuran gwamnati.
Wannan mataki ya bude kofa ga barazana ga sauran sarakunan da ke nuna ra’ayi ko suka ga gwamnati, musamman a matakin jiha.
Masarautu da dama sun shiga rikici, wasu sakamakon sabanin siyasa ko matsalolin cikin gida.
A wasu lokuta, gwamnoni na amfani da ikon su wajen rage yawan masarautu, kamar yadda aka gani a Kano da Kaduna, don rage karfin sarakuna ko kuma ladabtar da wadanda ba sa tafiya da su.
A bangare guda, wasu masu sharhi na ganin cewa rage tasirin sarakuna na nuni da kokarin cusa siyasa wajen murkushe tasirin masarautun gargajiya da ra’ayoyin da ke adawa da gwamnati.
Kwance rawunnan sarakuna sarakuna a Arewacin Najeriya na barazana ga tsarin masarautun gargajiya da kuma mutuncin da suke da shi a idanun al'umma, yana kuma tayar da muhawara kan rawar da ya dace su taka a siyasar zamani.
Galadiman Kano: Yan siyasa sun ziyarci Aminu Ado
Kun ji cewa wasu yan siyasa da sarakuna sun zabi zuwa fadar Aminu Ado Bayero bayan rasuwar Galadiman Kano.
Mafi yawansu sun kauracewa fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II saboda wasu dalilai na karan kansu.
Mutuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi ta jefa al’umma cikin jimami da alhini duba da girman dattijon a gare su da ma jihar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng