'Dan Karota Ya Mutu har Lahira bayan Wurgo Shi daga Saman Tirela a Kano

'Dan Karota Ya Mutu har Lahira bayan Wurgo Shi daga Saman Tirela a Kano

  • Wani jami’in hukumar KAROTA, Yahaya Isma’il Idris, ya rasu bayan wurgo shi daga cikin wata babbar mota a Kano a safiyar Alhamis
  • Rahotanni sun ce direban motar ya gudu ne bayan an nemi takardun kaya, sannan aka jefo jami’in daga cikin motar a yayin da take tafiya
  • ‘Yan sanda sun kama direban da fasinjoji biyu da ke tare da shi, kuma ana cigaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a birnin Kano inda jami’in hukumar kula da zirga-zirgar abubuwan hawa ta jihar (KAROTA), Yahaya Isma’il Idris, ya rasa ransa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Yahaya Isma'il Idris ya rasu ne sakamakon wurgo shi daga cikin wata babbar mota da ke tafiya da aka yi.

Karato
An wurgo dan Karota daga saman mota a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a X ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a kan titin Maiduguri da ke cikin birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa Yahaya Idris ya tsaya ne don binciken wata mota mai lamba BWR 457 XC, cike da kaya, amma hakan ya jawo rikici da ya yi sanadin rasuwarsa.

Yadda aka wurgo dan KAROTA a tirela

Rahoton Leadership ya nuna cewa dan KAROTAN ya dakatar da motar ne don duba takardun kaya da take ɗauke da su, amma direban bai gabatar da kowacce takarda ba.

Bayan haka ne jami’in ya shiga cikin motar domin ci gaba da bincike. Amma ba da jimawa ba direban ya ja motar da gudu.

An bayyana cewa a lokacin da suka kai kusa da gadar Muhammadu Buhari, sai aka jefo dan Karota Yahaya daga cikin motar.

Rahotanni sun nuna cewa Yahaya ya samu munanan raunuka inda aka garzaya da shi zuwa asibitin Murtala Muhammad, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An kama direban da ya wurgo jami'in KAROTA

An bayyana wanda ake zargi da tuka motar a mastayin Yakubu Abdulsalam, ɗan shekara 25 daga ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.

Fasinjojin da ke cikin motar sun hada da Tunde Momodu, ɗan shekara 31 daga jihar Edo da Sagir Yusuf, ɗan shekara 21 daga ƙaramar hukumar Bichi a Kano.

Karota
Ana bincike bayan mutuwar dan Karota a Kano. Hoto: Zagazola Makama
Asali: UGC

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cafke mutane ukun, inda take ci gaba da bincike don gano yadda aka kitsa wannan mummunan aiki.

Lamarin ya jefa al’ummar Kano cikin alhini, inda ake kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci da ɗaukar matakin da ya dace.

'Dan daba Baba Beru ya mutu a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani dan daba mai suna Baba Beru.

Rahotanni sun nuna cewa Baba Beru ya shahara da sace sace da barazana ga rayuwar al'umma kafin ya hadu da ajalin shi a jihar Kano.

Legit ta rahoto cewa an harbi Baba Beru ne a wata arangama da aka yi da 'yan sanda yayin da 'yan daba suka yi kokarin kwatar shi daga hannun hukuma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng