Hakeem Baba Ahmed: Abubuwan da Ya Kamata Su Hana Tinubu Takara a 2027
- Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya buƙaci Tinubu da ya hakura da takara a 2027 domin bai wa sababbin hannu damar jagoranci
- Ya ce hakan zai ba Tinubu damar kafa kyakkyawan tarihi, yana mai gargadin cewa tsunduma cikin siyasar 2027 a yanzu na iya hana nasarar mulkinsa na farko
- Dr. Baba-Ahmed ya soki salon shugabancin Tinubu, yana cewa yana da alaka da rashin jin daɗin al’umma, rashin tsari da kuma salon shugabancin nuna wariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mashawarci na musamman a fadar shugaban ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya hakura da takara a 2027.
Ya ce hakan zai ba Tinubu damar kafa ingantaccen tarihi da sauya tsarin siyasar ƙasa zuwa hanya mai tsafta, haɗin kai da cigaba.

Asali: Twitter
A cikin wata wasiƙa da Daily Trust ta fitar, Baba-Ahmed ya roƙi Tinubu da ya yi tunani mai zurfi kan barin tarihi mai kyau a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bukaci Tinubu ya hakura da takara a 2027
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa mafi kyawun abin da ya kamata Bola Tinubu ya yi shi ne hakura da takara a 2027 domin ba matasa damar jagoranci.
Ya bayyana cewa:
“Ka hakura – ba domin abokan hamayya ba, domin ba ‘yan Najeriya masu kuzari da hangen nesa dama.
Zai zama babbar nasara idan kai da jam’iyyarka kuka bai wa sababbin jini damar shugabanci,”
Ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ya yi la’akari da irin tarihi da zai bari da yadda tarihin ƙasa zai tuna da shi.
Maganar fara kamfen zaben 2027 tun yanzu
Tsohon mashawarcin ya yi gargadi cewa tsunduma cikin shirye-shiryen siyasar 2027 tun yanzu na iya sa a rasa nasarorin mulki da kuma goyon bayan jama’a.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce:
“Za ka iya cimma abubuwa da dama a cikin shekara biyu, amma idan ka fara maida hankali kan zaɓe, za ka iya rasa nasarar mulki da kuma amincewar jama’a,”
Ya ce Tinubu na da damar sauya rayuwar talaka idan ya mayar da hankali, yana mai cewa:
“Idan ka sake lashe zaɓe ba tare da gyara ba, za ka ƙara shekaru huɗu ba tare da tsinana komai ba. Idan ka sha kaye, tarihin ka zai ɓaci nan take.”
Hakeem Baba-Ahmed ya soki salon mulkin Tinubu
Baba-Ahmed ya bayyana cewa salon mulkin Tinubu ya ware shi daga sanin halin da jama’a ke ciki da kuma mutanen da za su taimaka masa ya samu nasara.
Ya soki salon rabon mukamai da Tinubu ke bi, ya ce bai nuna haɗin kai ba, tare da zargin gwamnatin da rashin tsari wajen bayani da hulɗa da al’umma.
Ya ƙara da cewa yawan masu magana da yawun gwamnati na rikita mutane maimakon su bayyana manufofin gwamnati yadda ya kamata.

Asali: Facebook
Tinubu ya gana da Fubara a London
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan Rivers da aka dakatar, Simi Fubara.
Gwamna Fubara ya hadu da Bola Tinubu ne a birnin London domin tattauna lamuran da ke da alaka da dakatar da shi.
Rahotanni sun nuna cewa akwai alamar Bola Tinubu zai shirya wani taro da jagororin jihar Rivers domin duba yiwuwar dawo da Fubara ofis.
Asali: Legit.ng