Ana Maganar Sauya Sheka, Kwankwaso Ya Hadu da El Rufa'i a Abuja

Ana Maganar Sauya Sheka, Kwankwaso Ya Hadu da El Rufa'i a Abuja

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da Rabiu Musa Kwankwaso, sun gana a Abuja yayin da ake ta rade-radin sauya sheƙar jagoran NNPP
  • An ga El-Rufai da ɗansa suna gaisawa da Kwankwaso bayan idar da sallar Juma’a a wani masallaci a Abuja, kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Duk da cewa a masallaci suka hadu, ganin su tare ya dauki hankali da ƙara ƙarfafa jita-jitar cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka kafin zabe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da ake magana kan yiwuwar sauya sheƙar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP zuwa APC, an hango Kwankwaso tare da Malam Nasir El-Rufai a Abuja.

Rahotanni sun ce El-Rufai da ɗansa, Hon. Bello El-Rufai, sun gana da Kwankwaso bayan sallar Juma’a a wani babban masallaci a birnin tarayya, Abuja, a ranar Juma’a.

KWankwaso
Kwankwaso ya hadu da El-Rufa'i a masallacin Juma'a. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar the Nation ta rawaito cewa musabaha da gaisuwar da suka yi ta ƙara hura wutar jita-jitar cewa Kwankwaso yana shirye-shiryen sauya sheka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin tsohon gwamnan, Saifullahi Hassan ya wallafa hotuna a shafin X, ya nuna ya yi sallah ne a masallacin Maitaima a Abuja.

Cikin tawagar Madugun akwai Shehu M. Bello da aka fi sani da Shehun Gari wanda ya na cikin shugabannin jam'iyyar NNPP na kasa.

Me haduwar Kwankwaso da El-Rufa'i ke nufi?

Al'ummar Najeriya, musamman 'yan Arewa sun fara mayar da hankali kan duk wani motsi da Kwankwaso ya yi tun da aka fara rade radin zai koma APC.

Sai dai haduwar shi da El-Rufa'i za ta iya zama koma baya ne ga rade radin komawar Kwankwaso APC, duk da cewa haduwarsu a masallaci ba lallai ta kasance tana da alaka da siyasa ba.

KWankwaso
Haduwar El-Rufa'i da Kwankwaso ta karfafa rade radin sauya sheka. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Rade radin komawar Kwankwaso APC

Tun kafin ganawar jita-jita ta yi yawa kan cewa Kwankwaso ya kammala yarjejeniya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin komawa APC.

Rahotanni sun bayyana cewa Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya za su iya ƙarfafa APC, musamman ganin yadda ake shirin fuskantar zaɓen 2027 mai zuwa.

Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa komawar Kwankwaso zuwa APC za ta zama babbar nasara ga Tinubu wajen neman tazarce a zaɓe mai zuwa.

Ganawar ta karfafa zargin shirye-shiryen siyasa

Masu lura da al’amuran siyasa sun bayyana cewa ganin El-Rufai da Kwankwaso tare a lokaci irin wannan na kara ƙarfafa zato game da wasu manyan sauye-sauye a fagen siyasar Najeriya.

Leadership ta wallafa cewa haɗuwa tsakanin manyan ‘yan siyasa kan zama wani shiri na ƙarfafa jam’iyya ko samar da sababbin haɗin gwiwa.

Sai dai, babu wata sanarwa daga ɓangarorin biyu dangane da abin da suka tattauna ko wani hukunci da aka cimma a ganawar.

Tsagin NNPP ya nemi sulhu da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa tsagin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya yi magana bayan wasu 'yan majalisun jam'iyyar sun koma APC.

Shugaban tsagin NNPP a jihar Kano, Mas’ud El-Jibril Doguwa ya daura laifin sauya shekar 'yan jam'iyyar a kan 'yan Kwankwasiyya.

Mas’ud El-Jibril Doguwa ya ce duk da abin da ya faru, yana shirye domin yin sulhu da bangaren Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng