Tsagin NNPP Ya Nemi Sulhu da Kwankwaso bayan Rasa 'Yan Majalisa a Kano

Tsagin NNPP Ya Nemi Sulhu da Kwankwaso bayan Rasa 'Yan Majalisa a Kano

  • Shugaban tsagin NNPP a Kano, Mas’ud El-Jibril Doguwa ya bayyana cewa za su yi taron gaggawa sakamakon ficewar jiga-jigan jam’iyyar zuwa APC
  • Mas’ud El-Jibril Doguwa ya dora alhakin ficewar mambobin jam’iyyar ga tafiyar Kwankwasiyya, yana zargin su da kawo rashin haɗin kai a jam’iyyar
  • Sai dai duk da haka, ya ce NNPP za ta ci gaba da kasancewa cikakkiyar jam’iyya mai zaman kanta, kuma kofa a buɗe take domin sasantawa da jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsagin NNPP reshen jihar Kano ta shiga rudani bayan ficewar wasu jiga-jigan jam’iyyar zuwa APC a makon da ya wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, Kabiru Alhassan Rurum, da Aliyu Madakin Gini da wasu da dama ne suka sauya sheƙa zuwa APC.

Kwankwaso
Tsagin NNPP ya ce zai yi sulhu da bangaren Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Shugaban tsagin NNPP a Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya bayyana wa jaridar PUNCH cewa suna shirin gudanar da taron gaggawa domin fuskantar wannan ƙalubale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masud Doguwa ya daurawa Kwankwasiyya laifi

Doguwa ya bayyana cewa sauya sheka ba sabon abu ba ne a gare su, yana mai daura laifin kan ɓangaren Kwankwasiyya bisa rashin amincewa da shugabancinsa.

Ya ce tun lokacin da ya hau kujerar shugabancin jam’iyyar, ya nemi haɗin kai amma ɓangaren Kwankwasiyya suka ƙi mara masa baya wajen cigaban jam’iyya.

Haka kuma, Doguwa ya zargi Kwankwasiyya da nuna bambanci da rashin adalci ga mambobin jam’iyyar wanda hakan ya jawo ficewar mutane da dama.

Doguwa ya fadi makomar NNPP a siyasance

A cewar Doguwa, ba gaskiya ba ne cewa ɓangarensa yana aiki da APC, yana mai jaddada cewa NNPP jam’iyya ce mai cikakken ‘yanci da adalci.

Ya ƙara da cewa ɓangaren su shi ne sahihin shugabancin da hukumar INEC ta amince da shi a jam’iyyar.

Doguwa ya bayyana cewa sun buɗe ƙofa don sasantawa da ɓangaren Kwankwaso domin sake gina jam’iyyar tare da shirin fuskantar zaɓen 2027.

Shirin NNPP na fuskantar zaɓen 2027

Shugaban jam’iyyar ya ce ana ci gaba da tattaunawa a shirin daidaita jam’iyyar tare da ƙokarin kara yawan mambobi kafin babban zaɓe mai zuwa.

Dangane da ficewar ‘yan siyasa zuwa APC, Doguwa ya ce sauya sheƙa al’ada ce a siyasa, yana mai cewa shahararrun ‘yan siyasa a Najeriya sun taɓa canza jam’iyya.

Kawu Sumaila
An zargi Kwankwasiyya da jawo ficewar Kawu Sumaila daga NNPP. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Twitter

2027: Fadar shugaban kasa ta caccaki Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi magana kan sauya shekar da gwamnan Delta da wasu jiga jigan jam'iyyar PDP suka yi a makon da ya wuce.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce masu kokarin mara baya wa Atiku Abubakar domin kalubalantar shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa sun watse.

A karkashin haka, fadar shugaban kasa ta ce kamar yadda Atiku Abubakar ya sha kaye a zabukan baya, haka zai kara shan kaye a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng