Trump Ya Fusata, Ya Yi Ƙarin Haske kan Jita Jitar Cewa Suna Fama da Ƙarancin Makamai

Trump Ya Fusata, Ya Yi Ƙarin Haske kan Jita Jitar Cewa Suna Fama da Ƙarancin Makamai

  • Shugaba Donald Trump ya yi martani mai zafi game da rahotanni da ake yaɗawa kan makaman Amurka a yakin da ake yi da Iran
  • Trump ya yi gargadin cewa jami'an da suka fitar da bayanan sirri kan karfin sojin Amurka za su fuskanci bincike da hukuncin daurin zaman gidan yari mai tsawo
  • Duk da rahotannin da ke nuna yakin Iran ya rage wasu makaman Amurka, Pentagon ta ce har yanzu kasar na da karfin soja kuma tana kara samar da makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da rahoton cewa yana fama da karancin makamai.

Trump ya musanta rahotannin da ke cewa kasar na fama da rashin makaman soja a yakin da ake yi da Iran.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Shugaba Trump ya yi magana kan batun karancin makaman Amurka

Trump ya ƙaryata maganar ƙarancin makamai a Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Alhamis, Trump ya ce ikirarin cewa Amurka ta fara rasa makamai saboda yakin da ake yi da Iran ba gaskiya ba ne.

Shugaban ya jaddada cewa har yanzu Amurka na da manyan tarin makamai saɓanin rahotanni da ake yadawa.

Ya ce Amurka na da makamai masu yawa, musamman wasu nau'o'i, sannan ana ci gaba da kera sababbi tare da kai su cikin kasar idan bukatar hakan ta taso.

Trump ya kuma yi alkawarin daukar tsauraran matakai kan duk wanda ya fitar da bayanan sirri game da karfin sojin Amurka zuwa kafafen yada labarai.

A cewarsa, ana ci gaba da farautar wadanda suka fitar da irin wadannan bayanai, kuma gwamnatinsa za ta nemi a yanke musu hukuncin daurin zaman gidan yari na dogon lokaci idan aka same su da laifi.

Kalaman Trump sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan matsayin tarin makaman Amurka bayan watanni ana fafatawa da Iran, inda aka yi hare-hare da dama duk da dakatarwar fada da aka taba yi.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi zabin Amurka tsakanin sulhu da yaki a Iran

Rahotanni daga wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa yakin ya rage wasu muhimman makaman Amurka, musamman makamai masu linzami masu dogon zango da ake amfani da su wajen kai hare-hare.

Cibiyar nazarin tsaro ta CSIS ta kiyasta cewa zuwa karshen watan Yuli, yawan makaman Patriot da Amurka ke da su ya ragu sosai idan aka kwatanta da adadin da kasar ke da shi kafin barkewar yakin.

Sai dai Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ci gaba da musanta cewa karfin sojinta ya ragu, yayin da Ministan Tsaro Pete Hegseth ya bayyana rahotannin karancin makamai a matsayin labarin da aka kirkira.

Hegseth ya kuma bukaci Majalisar Dattawan Amurka ta amince da dala biliyan 87 domin sake cike rumbun makamai, samar da sababbin kayan soja da kuma tallafa wa jami'an tsaro.

A lokaci guda, Amurka na ci gaba da bai wa Ukraine makaman Patriot domin yakin da take yi da Rasha, lamarin da ya kara jawo tambayoyi kan yadda za a iya daidaita bukatun bangarori daban-daban.

Masana harkokin soja sun bayyana cewa maye gurbin manyan makaman zamani na iya daukar shekaru saboda tsawon lokacin kerawa da isar da su, amma gwamnatin Trump ta ce tana kara yawan samar da makamai.

Kara karanta wannan

Rahoto daga Isra'ila ya tona asirin yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya kan Iran

Mashigar Hormuz: Iran ta gindaya sharuda

A wani labarin, an ji cewa Iran ta yi magana kan sake bude mashigar Hormuz wadda ta rufe sakamakon yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Tehran ta bayyana cewa ta cimma matsaya da Oman kan hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.

Hakazalika Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta ikirarin Donald Trump cewa ana tattaunawar cimma yarjejeniya da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.