Kano: Bayan Shekaru 2, Hukuncin Kisa Ya Hau kan Matashi da Ya Kashe Matar Mahaifinsa

Kano: Bayan Shekaru 2, Hukuncin Kisa Ya Hau kan Matashi da Ya Kashe Matar Mahaifinsa

  • Wata kotu da ke Kano ta yanke wa Sagiru Rijiyar-Zaki hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe matar mahaifinsa da 'yar uwarsa
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, Amina Adamu-Aliyu, ta ce an tabbatar da laifinsa bayan an gabatar da hujjoji da suka tabbatar da kisan
  • Lauyan gwamnatin jihar, Barista Lamido Abba-Sorondinki, ya ce laifin ya faru a Rijiyar Zaki, kuma ya gabatar da shaidu biyu da hujjoji
  • Sagiru ya musanta laifin da aka zarge shi da shi, inda lauyansa Barista Mubarak Abubakar ya gabatar da shi a matsayin mai bada shaida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wata babbar kotu a Kano ta yanke wa matashi hukuncin kisa bayan shafe shekaru biyu ana shari'a.

Kotun ta yanke hukuncin kan Sagiru Rijiyar-Zaki mai shekara 22 hukuncin kisa ta rataya saboda kashe mahaifiyarsa da 'yar uwarsa.

An yankewa matashi hukuncin kisa a Kano
Kotu a Kano ta yanke wa matashi hukuncin kisa kan zargin kisan mahaifiyarsa da ƴar uwarsa. Hoto: Legit.
Asali: Original

An tabbatar da laifinsa na kisan kai bayan kotu ta ce ya daba wa mahaifiyarsa Rabi’atu Sagir wuka, sannan ya shake kanwarsa, Munawara da mayafi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa a Bauchi

A kwanakin nan, Legit Hausa ta ruwaito cewa an kama wani matashi a jihar Bauchi da zargin kisan mahaifiyarsa.

Ana zargin wani matashi, Safiyanu Dalhatu ya hallaka mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi, lamarin da ya jefa al’umma a firgici da jimami.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wanda ake zargi tare da kwace tabaryar da ya yi amfani da ita wajen aikata wannan aika-aika.

An yanke hukuncin kan matashin Kano da ya kashe matar mahaifinsa
Kotu a Kano ta yanke wa matashi hukuncin kisa kan kisan kishiyar mahaifiyarsa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Hukuncin kisan da kotu ta yanke a Kano

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta yanke hukunci cewa masu kara sun tabbatar da laifin Sagiru ba tare da wata shakka ba.

Tun da farko, lauyan gwamnati Barista Lamido Abba-Sorondinki ya ce lamarin ya faru ne a ranar 7 watan ga Janairun 2023.

Lauyan ya kuma kawo shaidu biyu domin tabbatar wa kotu gaskiyarsa a shari'ar.

Ya ce, da misalin ƙarfe 8:00 na dare, a Rijiyar-Zaki, Sagiru ya kashe matar mahaifinsa mai suna Rabiatu, ta hanyar caka mata sukul direba a wuya bayan wata rashin jituwa.

Haka nan kuma ya shake ’yar uwarsa, Munawwara, da mayafinta wanda shi ma ya yi sanadiyyar ajalinta, kamar yadda rahoton Punch ya ruwaito.

A cewar mai gabatar da ƙara, laifin ya saɓa da tanadin Sashe na 221(a) na Dokar Hukunta Laifuffuka ta Jihar Kano ta shekarar 1991.

Lauya mai kare wanda ake zargi, Mista Mubarak Abubakar, ya gabatar da wanda ake tuhuma domin ya bayar da shaida a kansa.

Kotu ta yi hukunci kan kudin kananan hukumomi

Mun ba ku labarin cewa babbar kotun Kano ta haramtawa Babban Bankin CBN da wasu hukumomin tarayya riƙe kuɗin hananan hukumomin jihar Kano 44 da ke jihar.

Alkalin kotun, mai shari'a Musa Ibrahim Karaye ne ya yanke wannan hukuncin ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025.

Lauyan ƙananan hukumomin ya ce wannan nasara ta al'ummar Kano ce yayin da APC ta bayyana aniyarta na ɗaukaka ƙara kan shari'ar domin adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.