Matsayar LP, PDP da NNPP kan Shirin Hadaka a 2027 bayan El Rufai Ya Koma SDP
Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, ana hasashen jam'iyyun adawa za su yi haɗaka domin samun mulki a sauki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Hakan bai rasa nasaba da abin da suke ganin salon mulkin Bola Tinubu ya gaza kawo sauyi a Najeriya.
Daga cikin jam'iyyun adawa da ake hasashen zasu iya haɗaka tun farko akwai PDP da NNPP da SDP da kuma LP.

Asali: Facebook
Shirin haɗaka ya karfafa bayan shigan El-Rufai SDP
Sai dai wasu daga cikin jam'iyyun sun samu rarrabuwar kawuna kan lamarin, suke ganin ba za su iya shiga hadakar ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu ko gani suke yi ba za su samu abin da suke so ba musamman idan suka gabatar da sharudan shiga hadakar.
Duk wannan kiran hadakar ya kara karfi ne bayan ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP.
Tun bayan ficewarsa, lamarin ke kara karfi wanda hakan ya sanya suke ganawa da ziyarce-ziyarce domin neman mafita.
1. Matsayar jam'iyyar PDP kan haɗaka
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta yi fatali da shirin haɗaka da ake magana bayan Atiku Abubakar ya shiga gaba domin shiga shirin.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP yana gaba-gaba wurin kokarin hadakar da ake shirin yi kafin PDP ta watsar da batun.
Gamayyar gwamnonin PDP sun yi taro a jihar Oyo inda suka yi watsi da maganar haɗaka da ake yi.
Gwamnonin sun ce sun fi karfin haɗaka da jam'iyyar da ko kansila ba ta shi watau SDP yayin da suke da gwamnoni har 11.

Asali: Twitter
2. Abin da SDP ta ce kan haɗakar jam'iyyu
Jam'iyyar SDP ta nesanta kanta daga tattaunawar hadaka da nufin kafa kawancen da zai kayar da APC daga mulki, cewar Daily Trust.
Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Araba Rufus Aiyenigba ya ce SDP ta sake jaddada aniyarta na zama ingantaccen dandalin ‘yan Najeriya da ke neman sauyi, amma ta yi watsi da batun hadewa da wata jam’iyya.
Ta ce tana nan daram a kan kudirinta na kyakkyawan mulki, hadin kan kasa da adalci tare da jaddada cewa za ta bude kofarta ga dukkan masu kishin kasa, amma ba ta hanyar hadewa da wata jam’iyya ba.
Ta ce:
“Jam’iyyar ta sabunta kudirinta na jagorantar gwagwarmayar tabbatar da adalci a cikin al’umma, rayuwa mafi inganci ga jama’a, cigaban kasa da ci gaba mai dorewa.
"Amma ta yi tsayin daka a kan matsayinta na ‘ba hadaka’ da kuma ‘ba sabon tsarin fahimta."

Asali: Facebook
3. Tunanin NNPP kan shirin haɗaka
Jigon NNPP, Buba Galadima ya jaddada cewa jam'iyyar ba za ta yi haɗaka da wata jam’iyya don samun mulki ba.
Buba Galadima ya ce NNPP jam'iyya ce mai akida da tsari, ya ce ba za su hada kai da wata ba saboda neman mulki.
Ya ce:
“Mu jam’iyya ce mai aƙida, mu jam’iyya ce mai tsari, ba ma shiga haɗaka da wasu kawai don mu samu mulki ko ta halin ƙaƙa."
"Mun gamsu da jam'iyyar da muke da ita, wata rana, za mu ƙarfafa jam’iyyar nan mu lashe zaɓen ƙasa."

Asali: Facebook
4. Maganar LP/Peter Obi kan haɗaka
Shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar Obidient Movement Worldwide, Yunusa Tanko, ya yi maganan kan batun komawar Peter Obi jam'iyyar SDP.
Yunusa Tanko wanda ya kasance na kusa da Obi ya bayyana cewa har yanzu mai gidansa ɗan jam’iyyar LP ne, daga nan har zuwa wani lokaci da za a iya samun wani sabon ci gaba.
Tanko ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar LP za su fito da matsayarsu cikin ƴan kwanaki, musamman dangane da hukuncin Kotun Koli da ya tuɓe Julius Abure daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Atiku ya dauki darasin 2027 daga wasan Arsenal
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa nasarar da Arsenal ta samu a gasar Zakarun Turai ta karfafa masa gwiwa.
Atiku na ganin wasan da ta ba Arsenal damar kai wa matakin kusa da na karshe a gasar, ya nuna muhimmancin dunkulewa da hada karfi waje guda.
Ya kara da cewa hakan ya kara masa kwarin gwiwa kan hadakar jam’iyyun da suka kuduri aniyar kwato mulki daga jam’iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng