An Jero Mutum 3 da PDP Za Ta Fatattaka domin Tsira daga Wargajewa kafin 2027
- Ɗan majalisar wakilai, Ikenga Ugochinyere ya ce gwamnoni biyu da ‘yan majalisa 40 na shirin ficewa daga PDP saboda rikice-rikicenta
- Ugochinyere ya bukaci PDP ta gaggauta korar Samuel Anyanwu da Ministan Abuja, Nyesom Wike, domin hana rugujewar jam’iyyar
- Ya bayyana cewa an kulla makirci domin dawo da Umar Damagum da Anyanwu a matsayin shugabanni a babban taron watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Ideato, Mista Ikenga Ugochinyere, ya shawarci PDP kan yadda za ta tsira da mutuncinta.
Ɗan majalisar ya ce gwamnoni PDP biyu da ‘yan majalisa 40 sun shirya ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Asali: Facebook
Ana hasashen gwamnoni 2 za su dawo APC
Da yake magana da manema labarai a Akokwa a Ideato ta Arewa a jihar Imo, Ugochinyere ya bukaci PDP ta jiga-jiganta su sallami wasu manya, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya kamata a kori Samuel Anyanwu da ministan Abuja, Nyesom Wike domin hana jam'iyyar lalacewa.
Ugochinyere ya nuna bakin cikinsa kan rikicin da ke ci gaba a PDP, yana cewa shugabannin jam’iyyar sun yi shiru maimakon daukar matakin warware matsalar.
Ya ce:
"Ina kuma sanar da ku cewa na tabbatar da cewa ‘yan majalisa 40 da aka zaba a PDP za su fice daga jam’iyyar nan da makonni masu zuwa.
"Ranakun da muke tsoro sun iso, mun yi kuka, mun yi fada, mun roki shugabannin PDP su tashi su ceci jam’iyyar, amma sun yi sakaci.
"Mun fada musu akwai masu kutse cikin jam’iyyar kamar Umar Damagum da Samuel Anyanwu, amma gwamnoni da masu ruwa da tsaki sun yi wasa da hakan."

Asali: Facebook
An jero wadanda ya kamata PDP ta kora
Ɗan majalisar ya ce idan ana neman mafita ga jam'iyyar PDP dole ne a rufe ido domin korar wasu daga cikinta saboda samun daidaito, The Guardian ta ruwaito.
A cewarsa:
"Idan ba su samu dama ba, za su hana taron. Wannan abu ne mai matukar bakanta rai. Ina kira ga mambobin NWC su dauki matakin gaggawa.
"Na daya, a kori Samuel Anyanwu da Nyesom Wike daga PDP. Wannan shi ne bukatar mafi yawan masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar a halin yanzu.
"Idan NWC ba ta iya korar wadanda ke lalata jam’iyyar ba kamar Damagum to, a kira taron NWC, a yi korar, komai tashin hankali da zai biyo baya, za a shawo kansa."
Shugaban PDP ya magantu kan zaben 2027
Kun ji cewa shugaban riko na PDP, Umar Damagum, ya bayyana cewa makomar kasar na hannun 'yan Najeriya, musamman a lokacin zaben 2027.
Damagum ya yi kira ga masu zaɓe su yi amfani da 2027 wajen rama abin da gwamnatin APC ta yi masu, na jefa su a cikin kunci.
Game da sauya shekar jiga-jigan PDP zuwa APC, Damagum ya bayyana matukar takaici, ya ce jam'iyyar ba ta yi wa jagororin laifin komai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng