Bayan Komawa APC, Gwamna Ya Fara Cin Karo da Matsalar Farko a Gwamnatinsa
- Gwamnatin Delta ta fuskanci koma baya, Harrison Gwamnishu, mai ba gwamna shawara kan matasa da kungiyoyin farar hula, ya ajiye aikinsa
- Gwamnishu ya bayyana a wasikar murabus dinsa cewa duk kokarinsa na shawo kan Gwamna Oborevwori game da matsalar tsaro da ya ci tura
- A cewarsa, rashin yanke shawara mai ma’ana daga gwamnati ya sa ya kasa ci gaba da aiki da amana da nagarta kamar yadda ya yi alkawari
- Ya kuma ce yana fatan murabus dinsa zai jao hankalin gwamnati kan muhimmancin magance matsalolin tsaro don amfanin al’umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Hadimi na musamman kan harkokin farar hula da wayar da kan matasa ga Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya ajiye aikinsa.
Tsohon hadimin mai suna Harrison Gwamnishu, ya ajiye aikinsa saboda matsalar tsaro da ta addabi jihar da ke Kudancin Najeriya.

Asali: Facebook
Hadimin gwamna Sheriff ya ajiye muƙaminsa
Harrison Gwamnishu ya bayyana haka a cikin wasikar murabus dinsa da ya wallafa a shafin X a jiya Juma'a 25 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnishu ya ce duk wani kokari na jawo hankalin gwamna da ya sauya fasali da halin da jihar ke ciki ya faskara.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta shirya daukar matakai na magance matsalar tsaro ba, lamarin da ya sa ya kasa yin aiki da gaskiya da amana.
Wasikar ta ce:
“Na yanke wannan shawara bayan nazari mai zurfi da jin takaici dangane da cigaban matsalar tsaro a al’ummarmu da na dade ina korafi akai.
“Duk da sakonnin waya da kira da na gabatar da takardun tsare-tsare don magance matsalar, dukkansu an yi biris da su, kuma gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Asali: Facebook
Musabbabin ajiye aikin Hadimin gwamnan Delta
Gwamnishu ya ce tun farko ya karbi muƙamin ne domin kare muradun al'umma amma kuma ya lura abubuwa sun ki daukar hanya yadda ya dace.
Ya ce:
“A matsayina na jagoran kare hakkin jama’a, na karɓi wannan mukami ne da kuduri na kare al’umma. Amma yawaitar matsalar tsaro da gazawar gwamnati ya gagara.
“Kudurina na kare rayuka da lafiyar al’umma bai gushe ba, amma matsalar tsaro ya kamata ta zama fifiko. Ina fatan murabus dina zai zama darasi ga gwamnati.
“Na gode da damarmakin da aka ba ni a lokacin aikina da kuma dangantakar da na kafa da abokan aiki da al’ummar jihar Delta gaba ɗaya.”
APC ta yi maraba da gwamnan Delta, Sheriff
A baya, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi maraba da sauya sheƙar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa cikinta.
Jam'iyyar ta ce sauya sheƙar da gwamnan ya yi, ta sanya yanzu jihar Delta za ta ba da cikakkiyar gudunmawa wajen cimma manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
An ce APC ta yi alƙawarin ga Gwamna Sheriff Oborevwori tare da sauran masu sauya sheƙar cikakken haɗin kan da ya dace domin samun nasara a zabuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng