Jam'iyyar NNPP Ta Jero Matakai 3 da Take Shirin Dauka game da Zaɓen 2027

Jam'iyyar NNPP Ta Jero Matakai 3 da Take Shirin Dauka game da Zaɓen 2027

  • Mai magana da yawun NNPP, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa suna nazarin yiwuwar ci gaba da zama a jam'iyyar ko kawance da Atiku Abubakar
  • Johnson ya ce sun fi yawaita yanke shawarar siyasa bayan rabin wa'adin mulki, inda ya ce ranar 29 ga Mayun shekarar 2025 ce za ta dace da hakan
  • Ya kara da cewa duk da rade-radin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai-ci da ake yadawa, babu wani abu da aka tabbatar yanzu haka a zahiri
  • Johnson ya ce akwai zabuka uku: ci gaba da zama a NNPP, hada kai da Atiku da wasu ko kuma shiga kawance da jam’iyyar APC mai mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya magantu kan matsayarsu game da zaben 2027 da ake tunkara.

Johnson ya bayyana cewa suna duba yiwuwar cigaba da zama a jam'iyyar NNPP ko kuma shiga kawance da Atiku Abubakar da wasu, ko kuma hada kai da APC.

NNPP ta fadi shirinta kan zaben 2027
Jam'iyyar NNPP ta ce ta shirya duba yiwuwar samun matsaya kan zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Rabi'u Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta yi magana kan zaben 2027

Ladipo Johnson ya tabbatar da cewa lallai suna tantance wadannan zabuka na siyasa a halin yanzu, cewar rahoton Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"To, abin da zan fada a yanzu shi ne, a NNPP, daga tarihinmu na Kwankwasiyya, muna jiran rabin wa'adin gwamnati kafin siyasa ta fara tukuna.
"Eh, muna tattaunawa kuma mun dade muna haka amma kamar yadda na fada da farko, ba zan bayyana wadanda muke magana da su ba.
"Za ku tuna da labaran da ake yadawa cewa Sanata Kwankwaso zai koma APC nan ba da jimawa ba, wannan dai halin siyasa ne kawai."
NNPP tana tunanin hada kai da Atiku ko maja da APC
Jam'iyyar NNPP ta fadi yiwuwar hada kai da Atiku ko marawa Tinubu baya a 2027. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Shawarar NNPP ga al'ummar Najeriya kan 2027

Johnson ya shawarci al'umma su yi hakuri da yada labaran karya inda ya tabbatar da cewa su jira daga bakin jam'iyyar NNPP.

Ya tabbatar da cewa akwai matakai uku da su ke tunanin ɗaukar daya daga ciki kuma tabbas hakan zai faru, kamar yadda mai amfani da X, @Imranmuhdz ya wallafa.

Ya kara da cewa:

"Kamar yadda na fada, mutane suna kokarin yada labaran da za su amfane su, amma za ku ji daga gare mu nan kusa.
"Muna da zabuka uku a gabanmu: ci gaba da zama a NNPP, ko kawance da Atiku da wasu, ko kuma kawance da jam’iyyar APC mai mulki.
"Ba na cewa kowane daga cikin wadannan shi ne zabi yanzu, amma wadannan su ne zabukan da za su iya faruwa."

An yi wa Kwankwaso da Abba tayin APC

Mun ba ku labarin cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana cewa za su marabci Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf.

Bashir ya ce APC na shirin tarbar Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir da ma sauran mambobin jam'iyyar NNPP na jihar Kano baki daya.

Hakan na zuwa ne bayan Sanata Kawu Sumaila da kusan dukkan jiga-jigan PDP a Delta sun koma APC bayan wani taro da aka yi a gidan gwamnati da ke Asaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.