Trump na Farautar Wanda Ya Tona Asirin Makaman Amurka a Yakin Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotannin da ke cewa rundunar ƙasar na fuskantar ƙarancin makamai, musamman makamai masu linzami masu cin dogon zango
- Trump ya ce Amurka na da dimbin makamai kuma ana ci gaba da kera wasu tare da tura su ƙasar gwargwadon buƙata, yayin da Iran ta ce tana da isassun makamai da za ta iya tunkarar duk wata barazana
- Shugaban Amurkan ya kuma yi barazanar ɗaukar tsauraran matakai kan mutanen da ya zarga da fallasa bayanan sirri game da yanayin makaman sojojin ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya musanta rahotannin da ke cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin makamai sakamakon yawan amfani da su a yaƙin da ake yi da Iran.
Shugaba Trump ya kuma yi barazanar hukunta mutanen da ake zargi da fallasa bayanan sirri game da yawan makaman da Amurka ke da su.

Kara karanta wannan
Trump ya fusata, ya yi ƙarin haske kan jita jitar cewa suna fama da ƙarancin makamai

Source: Facebook
Barazanar daTrump ya yi
Rahoton da BBC ta wallafa ya nuna cewa shugaba Donald Trump ya nuna fushi kan yadda wasu bayanai game da makaman sojojin Amurka ke fitowa fili.
Ya ce mutanen da yake zargi da fallasa irin waɗannan bayanai ana farautarsu, yana kuma barazanar neman a yanke musu hukuncin zaman gidan yari na dogon lokaci.
Ya kuma kai hari kan rahoton da aka fitar yana mai bayyana irin wannan rahoto a matsayin abin da ya yi kama da cin amanar ƙasa.
Trump ya kuma jaddada cewa yana matuƙar farin ciki da aikin da Pete Hegseth ke yi a matsayin ministan yakin Amurka.
Yawan makaman Amurka
Rahoton WSJ ya nuna cewa ba a bayyana ainihin adadin makaman linzami da Amurka ke da su ba, saboda bayanan suna cikin sirrin tsaron ƙasa.
Sai dai wata cibiyar bincike kan harkokin tsaro ta (CSIS ta yi kiyasin cewa zuwa ƙarshen watan Yuli, Amurka na iya samun makamai masu linzami na Patriot tsakanin 759 da 827, daga kimanin 2,330 da take da su kafin rikicin.

Source: Getty Images
Cibiyar ta kuma yi kiyasin cewa Amurka ta riga ta yi amfani da kusan kashi 60 cikin 100 na makamai masu linzami na THAAD, waɗanda ake amfani da su wajen kakkabo hare-haren makamai masu linzami.
Abubuwa sun fashe a Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa an ji fashewar abubuwa guda biyu a Kudancin Iran, inda rahotanni suka ce fashewar na da alaƙa da wani farmaki da sojojin ruwan Iran suka kai kan wasu abubuwan da aka bayyana a matsayin "maƙiya".
Wani kamfanin dillancin labarai a Iran ya ce an ji fashewar ne a tsibirin Qeshm da misalin ƙarfe 9:40 na dare, yayin da majiyoyin suka ce sojojin ruwan Iran sun gudanar da wani samame kan abubuwan da suka kira maƙiya.
Sai dai wani jami'in lardin Hormozgan ya ce ba a samu rahoton wani hari ko wata illa a tsibirin Qeshm ko birnin Bandar Abbas ba, yayin da hukumomi ke gudanar da bincike kan musabbabin fashewar.
Asali: Legit.ng
