Dalilin da Ya Sa NRS ke Ganin Cire Tallafin Man Fetur Shi ne Mafi Alheri ga Yan Najeriya

Dalilin da Ya Sa NRS ke Ganin Cire Tallafin Man Fetur Shi ne Mafi Alheri ga Yan Najeriya

  • Shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, Zacch Adedeji ya ce cire tallafin man fetur shi ne mafi alherin mataki da ya taba faruwa a Najeriya
  • AdedejinYa yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki
  • Adedeji ya kuma kalubalanci masu shirin neman takarar shugaban kasa a 2027 da su bayyana abin da za su yi daban domin magance matsalolin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mafi kyawun abu da ya faru da Najeriya.

Mista Adedeji ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ya dauka na cire tallafin tun a ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki a 2023.

Shugaban hukumar NRS.
Shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, NRS, Zacch Adedeji a ofishinsa a Abuja Hoto: Zacch Adedeji
Source: UGC

Zacch Adedeji ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television.

Kara karanta wannan

"Ban yabo don a so ni" Gwamna Sule ya cire tsoro ya ragargaji Shugaba Tinubu

Ya ce wasu daga cikin nasarorin tattalin arzikin da gwamnati ta samu sun samo asali ne daga cire tallafin mai.

Adedeji ya kare cire tallafin mai

Shugaban NRS ya ce tsarin tallafin man fetur ba mI dorewa ta fuskar kudi, kuma ya yi wa tattalin arzikin kasar illa duk da cewa an shafe shekaru ana amfani da shi.

“Dukkan sakamako masu kyau da zan lissafa nan gaba sun samo asali ne daga wannan mataki na jarumtaka na cire tallafin mai.
"Don haka ba kuskure ba ne; shi ne mafi alherin abu da ya faru da wannan kasa. Tallafin mai mugun abu ne kuma ya dade yana tare da Najeriya,” in ji shi.

Adedeji ya ce Tinubu ya karbi tattalin arzikin da ke fama da matsalar tallafin man fetur da ba za a iya ci gaba da daukarsa ba, bangaren mai da ke fuskantar koma baya da kuma karancin hanyoyin tara kudaden shiga daga haraji.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika saƙo cikin kaɗuwa da aka tabbatar da rasuwar babban malami a Najeriya

Ya ce saboda haka gwamnatin ta fara aiwatar da wasu manyan sauye-sauye domin magance matsalolin da suka dade suna addabar tattalin arzikin kasar, cewar rahoton Leadership.

Ya bukaci a duba tasirin sauye-sauyen

Shugaban NRS ya bukaci ‘yan Najeriya su rika tantance manufofin tattalin arzikin gwamnati bisa tasirinsu na dogon lokaci, maimakon yin hukunci bisa fushi da ɓacin rai.

Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun kawo sauyi mai muhimmanci a tsarin tattalin arzikin Najeriya, duk da cewa wasu masu sukar gwamnati ba su amince da hakan ba.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar NRS, Zacch Adedeji a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Adedeji ya kuma kalubalanci masu shirin neman takarar shugaban kasa a 2027 da su bayyana abin da za su yi daban domin magance matsalolin tattalin arzikin kasar idan aka zabe su.

“Abin da Shugaban kasa ke bukata yanzu shi ne goyon baya da yabo saboda ya nuna cewa shi dan kasa ne mai kishin kasa, ba dan siyasa kawai ba. Duk wanda ya ce zai zo ya yi takara, ku tambaye shi: ‘Me za ka yi daban?’”

Gwamna Sule ya yaba d cire tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce jihar yanzu tana karɓar N14bn zuwa N16bn a kowane wata, bayan cire tallafin man fetur.

Gwamnan ya ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262