Bayan Ganawa da Tinubu a Landan, Ana Zargin Gwamnan PDP Zai Sauya Sheka zuwa APC
- Ana hasashen cewa Gwamna Siminalayi Fubara na shirin daukar wasu matakai da za su kawo karshen rikicin siyasa a jihar Rivers
- Majiyoyi sun ce Fubara, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Landan, yana nazarin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
- Wannan ce ganawar Tinubu da Fubara ta farko tun bayan ayyana dokar ta baci a Rivers, kuma ana ganin gwamnan na neman sulhu ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Alamu na nuna cewa gwamnan Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, na shirin daukar wasu matakai da za su iya rage rikicin siyasa a jihar.
Wannan ya biyo bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu a Landan yayin tafiyarsa ta hutun kwanaki 18 a Turai, kamar yadda muka ruwaito.

Asali: Twitter
Fubara ya gana da Tinubu a Landan
Jaridar The Africa Report ta tabbatar da cewa Gwamna Fubara ne ya nemi wannan ganawar da shugaban kasa Tinubu, wanda ya fara mulki a watan Mayun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa ba a tabbatar da cikakken bayani kan zaman ba, amma wani babban hadimin Tinubu ya bayyana cewa Fubara ya amince da wasu sauye-sauye don magance rikicin Rivers.
Hadimin ya bayyana cewa:
“Ina mai tabbatar muku cewa Fubara ya gana da Shugaban kasa a sirrance makon jiya. Ya yi alkawarin canja ra’ayinsa kan wasu batutuwa domin a samu zaman lafiya."
Hadimin ya kara da cewa ana ci gaba da tattaunawa, kuma akwai alamun Fubara zai koma kujerarsa kafin wa'adin dakatarwar wata shida da aka yi masa ya cika.
Ana hasashen Fubara zai koma APC
Wani hadimi na daban ya bayyana cewa Fubara na duba yiwuwar ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa APC mai mulki don zama inuwa daya da Shugaba Tinubu.
“In har Fubara ya koma APC, hakan na nufin Tinubu zai fi samun karbuwa a Jihar Rivers a zaben 2027,” inji hadimin, yayin hira da wata jarida Faransanci.
Wasu hadiman shugaban kasa da wakilin Punch ya tuntuba sun ce ba su raka shugaban kasar wannan tafiya ba, don haka ba su halarci ganawar ba.
Wannan ne karon farko da shugaban kasa da gwamnan suka yi ido biyu tun bayan da Tinubu ya aiwatar da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 a ranar 18 ga Maris.
Shugaban kasa, wanda ya je Paris sannan London tun ranar 2 ga Afrilu, ya amince da ganawa da Fubara don warware rikicin siyasar da ke ci gaba da faruwa a Rivers.

Asali: Facebook
Abin da ake tunanin Fubara da Tinubu sun tattauna
Rahotanni sun ce sun tattauna ne kan yadda za a dawo da sahihin shugabanci a jihar da ke da arzikin man fetur.
Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan ganawar, amma wasu majiyoyi sun ce Fubara na iya komawa kujerarsa kafin dakatarwarsa ta kare a watan Satumba.
An kuma gano cewa tsohon ubangidansa na siyasa kuma ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, bai halarci zaman ganawar ba.
Duk da haka, ana sa ran Tinubu zai gana da Fubara, Wike da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar nan gaba kadan domin samo mafita ta dindindin ga rikicin siyasar Rivers.
Wike ya so raba Fubara da kujerar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ya so a ce an raba Siminalayi Fubara da kujerar gwamnan Rivers na har abada.
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya hana hakan, ta hanyar ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers, wanda a cewarsa ya ceci Gwamna Fubara.
Wike ya koka kan yadda Fubara ya ki ya nemi sasanci da shi, duk da rikicin siyasar da ke tsakaninsu yana ƙara ta'azzara.
Asali: Legit.ng