An Watsewa PDP, Mataimakin Atiku a Zaben 2023 Ya Watsar da Ita, Ya Koma APC
- Tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa da wasu jiga-jigan PDP sun koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- Sanata Okowa shi ne ya yi takara a matsayin mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 da ta gabata a karkashin PDP
- Okowa ya koma APC ne tare da wasu manyan jiga-jigan PDP a jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin Najeriya
- Hakan ya biyo bayan ficewar Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori wanda aka zaba a 2023 daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP, Ifeanyi Okowa ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Sanata Okowa shi ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 karkashin Atiku Abubakar a PDP.

Asali: Twitter
Gwamnan Delta ya koma APC daga PDP
Kwamishinan yada labarai, Charles Aniagwu, shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Laraba 23 ga watan Afrilun 2023, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aniagwu ya kuma tabbatar da ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori daga PDP zuwa APC.
Ya ce canjin jam’iyya zai taimaka wajen ci gaban jihar da tabbatar da walwalar al’ummar Delta.
Aniagwu Charles, ya tabbatar da sauyin jam’iyya na gwamnan da sauran jagororin PDP zuwa jam’iyyar APC.
Ya ce:
“Dole ne mu daidaita yadda muke shan ruwanmu, domin hakan zai taimaka wajen ci gaban jihar da karfafa tsaron al’umma.
"Don haka, muka yanke cewa barin PDP wajibi ne domin hada kai da gina jihar da kowane dan Delta zai yi alfahari da ita.”
Charles ya ce shugabanni da masu ruwa da tsaki sun yanke wannan shawara tare, kuma nan da mako mai zuwa za su fito da bayani a hukumance.
Ya ce:
“Da ikon Allah, a ranar Litinin mai zuwa, za mu fito da muhimmin bayani da zai tabbatar da shigarmu cikin jam’iyyar APC.”
Wannan mataki na nuna juyin juya hali a siyasar jihar Delta, wanda ka iya sauya tasirin jam’iyyun siyasa a yankin Kudu maso Kudu.

Asali: Facebook
Okowa ya bar PDP zuwa jam'iyyar APC
Sanarwar ficewar Okowa ta fito ne ranar Laraba a birnin Asaba a Delta, ta bakin Sanata James Manager, bayan taron awa shida a gidan gwamnati.
Manager ya ce jam'iyyar PDP ta rasa kusan dukan mambobinta a jihar da shugabannin daga sama har kasa, cewar Daily Post.
Ya ce:
"Dukkan mambobin PDP a jihar, ciki har da gwamna, tsohon gwamna Okowa, shugaban majalisa, shugabannin kananan hukumomi da sauransu, sun yanke shawarar shiga APC.
“Ba za mu ci gaba da zama a cikin jirgin da ke nitsewa ba."
Gwamna Eno ya musanta shirin komawa APC
Kun ji cewa gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno ya musanta labarin cewa yana shirin barin PDP zuwa jam'iyyar APC.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Aniekan Umanah shi ya musanta rade-radin cewa Gwamna Eno na shirin ficewa daga PDP zuwa APC.
Umanah ya bayyana cewa hadin gwiwar gwamnati ta kawo sauyi kamar 'Ibom Seaport' da gyaran muhalli da ci gaban al'umma baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng