Akpabio Ya Mayar da Biki, Ya Goyi bayan Tazarcen Gwamnan PDP

Akpabio Ya Mayar da Biki, Ya Goyi bayan Tazarcen Gwamnan PDP

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya nuna goyon bayansa ga tazarce Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom
  • Godswill Akpabio ya yabawa gwamnan kan yadda ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu duk da cewa yana PDP
  • Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa za su goyi bayan Umo Eno domin ya ci gaba da mulki a jihar mai arziƙin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nuna goyon bayansa ga takarar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom na PDP domin ya yi tazarce.

Godswill Akpabio ya bayyana goyon bayan ne a matsayin maida biki kan goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnan ya yi.

Godswill Akpabio
Akpabio ya goyi bayan tazarcen Gwamna Umo Eno Hoto: Godswill Obot Akpabio, Pastor Umo Eno
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka yi a jami'ar Uyo a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Godswill Akpabio ya samu wakilcin shugaban hukumar kula da harkokin majalisar tarayya, Saviour Enyiekere a wajen taron.

A ranar Talata, Gwamna Eno ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Gwamnan ya jaddada cewa shugaban ƙasan zai kammala shekaru takwas, tare da alƙawarin yin amfani da dukkan damar sa wajen tabbatar da hakan.

Akpabio ya goyi bayan tazarcen Gwamna Uno

Godswill Akpabio ya yaba da wannan mataki da gwamnan ya ɗauka, yana mai cewa Gwamna Eno ya kafa tarihi.

“Ranka ya daɗe, saboda abin da ka yi, ina mai tabbatar maka a matsayina na ɗan APC, kuma ina magana da yawun dattawan jam'iyyar, cewa za mu mara maka baya don samun wa’adin mulki na biyu."
“Za mu goyi bayanka a duk wani buri da kake da shi. Ka kafa tarihi ta hanyar zama gwamnan jam’iyyar adawa na farko da ya bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu domin ya tsaya takara a wa’adi na biyu."

- Sanata Godswill Akpabio

Gwamna Eno ya yi magana kan salon mulkinsa

Gwamna Umo Eno
Gwamna Umo ya ce yana tafiya da kowa a gwamnatinsa Hoto: Pastor Umo Eno
Asali: Twitter

Da yake magana kan siyasa, Gwamna Eno ya ce gwamnatinsa tana ƙoƙarin tafiya da kowa da kowa ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

"Tun daga lokacin da na hau mulki, na yi ƙoƙarin yin mulki wanda zai tafi da kowa da kowa. Na yi ƙoƙarin kawo zaman lafiya tsakanin shugabannin da suka gabata da waɗanda ke kan mulki a yanzu, domin mu samu zaman lafiya ba tare da rigima ba."

“Ba ma yawan rikici a tsakaninmu. Muna siyasa ta mutunta juna da girmamawa."
"Jam’iyya ba ita ce ke nuna waye mutum ba, kai ne kake zuwa cikin jam’iyya da halinka. Don haka, kar a yaudare ni cewa wata jam’iyya tafi wata. Jam’iyyun siyasa kawai suna bayyana wane ne kai."

- Gwamna Umo Eno

Tsohon sanata ya yi zarge-zarge kan Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya yi zarge-zarge kan Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Elisha Abbo ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawan ya takura masa saboda bai goyi bayansa ba.

Tsohon sanatan ya nuna cewa shugaban majalisar ya sanya an ƙi biyansa albashinsa na ƙarshe kafin ya bar majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng