Matasa Sun Juyawa Tinubu Baya, Sun Roƙi Gwamna Ya Nemi Kujerar Shugaban Ƙasa a 2027

Matasa Sun Juyawa Tinubu Baya, Sun Roƙi Gwamna Ya Nemi Kujerar Shugaban Ƙasa a 2027

  • Wasu matasa sun ayyana goyon bayansu ga Gwamna Seyi Makinde, sun bukaci ya fito takarar shugaban kasa a babban zaɓen 2027
  • A wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta fitar, ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da Makinde amma ta hango irin ci gaban da ya kawo a Oyo
  • Matasan sun faɗi hakan ne domin martani ga tsohon gwamna, Ayo Fayose, wanda ya ce Makinde ba shi da niyyar gwabza wa da Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Yayin da ake shirin tunkarar babban zaben 2027, matasa sun bukaci Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya fito takarar shugaban ƙasa.

Wata kungiyar matasa mai suna Progressive Youth for Makinde’s Presidency 2027 ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnan domin ya nemi mulkin Najeriya.

Gwamna Makinde.
Matasa sun ayyaka cikakken goyon bayansu ga Gwamna Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren kungiyar, Prince Christopher Odianarewo, ya fitar a karshen mako, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun yabi Gwamna Makinde

Ya ce salon shugabancin da Makinde ya gudanar a jihar Oyo mai cike da kawo sauyi ya samu karbuwa a wurin matasa da sauran 'yan Najeriya.

"Mun gamsu da irin gagarumin ci gaban da Gwamna Makinde ya kawo a fannonin lafiya, ilimi, tsaro, gidaje, hanyoyi, noma, abinci, ci gaban dan Adam, jagoranci, da zaman lafiya tsakanin addinai da kabilu.
"Wannan ne ya sa mu ke ganin ya cancanci mulkin kasa baki daya.”

- In ji Prince Christopher Odianarewo.

2027: Matasa sun yi martani ga Ayo Fayose

Matasan sun mayar da martani ne ga tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, wanda ya musanta cewa Makinde na ba shi da shirin neman kujarar shugaban ƙasa a 2027.

A wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a yau na Channels tv, Fayose ya ce Makinde ya musanta lamarin da kansa, yana mai cewa ba zai gwabza da dan uwansa bayerabe ba.

Fayose ya ce:

“Na tura masa fastar da na gani a dandalin sada zumunta da ke nuna yana sha’awar takarar shugaban kasa. Ya kira ni ya ce ba da yawunsa aka buga ta ba.
Gwamna Makinde.
Kungiyar matasa ta yi wa Fayose raddi Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Yadda matasa suka fara juyawa Tinubu baya

Sai dai kungiyar matasan ta bayyana cewa ba su taɓa cewa ta na da alaka da Makinde ko ya amince da bukatarsu ta neman takara a 2027 ba.

Matasan suka ce:

“Ba mu taɓa bayyana cewa muna da wata alaka kai tsaye ko ta bayan fage da Gwamna Makinde ba.
Mun fara wannan yunkuri ne a 2024 domin duba halin da jam’iyyar PDP ke ciki da kuma shirin ceto Najeriya daga hannun APC.”

Kungiyar ta ce tun daga shekarar 2015 Najeriya ke kara tabarbarewa karkashin mulkin jam'iyyar APC.

Ta jero koma bayan da aka samu a gwamnatin APC kamar faɗuwar darajar Naira, rashin tsaro na kara ta’azzara, farashin gidaje da karatu ya hauhawa, da sauransu.

Makinde ya nesanta PDP da haɗakar Atiku

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Makinde ya ce ba zai yiwu su shiga haɗakar ƴan adawa wacce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ke jagoranta ba.

Makinde ya bayyana cewa babu ta yadda za su shiga wannan haɗaka da ake ta surutu a kai saboda jam'iyyar PDP ba ta da masaniyar komai akai.

Ya ce gwamnonin PDP sun ɗauki matsaya ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a taron da suka yi a Ibadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262