"Ban da PDP": Gwamna Ya Fadi Masu Fafatawa da Gwamnatin APC a Zaben 2027

"Ban da PDP": Gwamna Ya Fadi Masu Fafatawa da Gwamnatin APC a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba zai kasance tsakanin jam'iyyar PDP da APC ba
  • Seyi Makinde ya bayyana cewa zaɓen zai kasance ne tsakanin ƴan Najeriya da jam'iyyar APc mai mulki
  • Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta tafka kuskure a zaɓen 2023, wanda hakan ne ya jawo mata rashin nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai kasance ne tsakanin ƴan Najeriya da jam’iyya mai mulki ta APC.

Gwamna Seyi Makinde
Gwamna Makinde ya tabo batun zaben shugaban kasa na 2027 Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Najeriya za su fafata da APC a 2027

Seyi Makinde ya bayyana cewa zaɓen ba zai kasance tsakanin APC da jam’iyyarsa, wato babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba.

Kara karanta wannan

"Na cancanci zama shugaban ƙasa," Gwamna ya yi bayanin shirinsa a zaɓen 2027

“Zaɓen 2027 ba zai kasance tsakanin PDP da APC ba, zai kasance ne tsakanin ƴan Najeriya da APC. Ku rubuta wannan maganar ku ajiye."

- Gwamna Seyi Makinde

Gwamna Makinde ya dora laifin tabarbarewar tattalin arziki da ƙara lalacewa tsaro a ƙasar nan a kan gwamnatin APC.

Ya bayyana cewa zaɓen mai zuwa zai zama lokacin yanke hukunci ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Gwamnan na Oyo ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta PDP ita ce fatan talaka, yana mai tabbatar da cewa PDP ba za ta sake kuskuren da ya sa ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

Gwamna Makinde ya faɗi kuskuren PDP a 2023

Yayin da yake nazari kan abin da ya faru a zaɓen da ya gabata, Makinde ya ce PDP ta yi babban kuskure lokacin da ta bai wa ƴan arewa uku manyan muƙamai.

Ya ce akwai kuskure a ba da muƙamin ɗan takarar shugaban ƙasa, shugaban jam’iyya na ƙasa, da kuma shugaban kwamitin kamfen na shugaban ƙasa a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnonin PDP sun bayyana matsayarsu kan hadaka don kayar da Tinuɓu

Ya ce ware ƴan kudu daga waɗannan manyan muƙamai uku ya sanya PDP ta yi wa kanta illa da kanta, wanda hakan ya haifar da rashin nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.

Seyi Makinde
Seyi Makinde ya ce PDP ta yi kuskure a zaben 2023 Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

A lokacin shirin zaɓen da ya gabata, Iyorchia Ayu daga Arewa ta Tsakiya ne shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar daga Arewa maso Gabas ne ɗan takarar shugaban ƙasa.

Sannan tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal daga Arewa maso Yamma shi ne shugaban kwamitin kamfen na Atiku.

"Ta ya za a tallata wannan takarar a faɗin ƙasa idan manyan muƙamai uku da suka jagoranci shirin zaɓen duka daga Arewa suka fito, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma?"

- Gwamna Seyi Makinde

Makinde ya yi maganar zama shugaban ƙasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi magana kan yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

Gwamna Makinde ya bayyana cewa yana da ƙwarewa da gogewar da ake buƙata domin zama shugaban ƙasan Najeriya.

Seyi Makinde ya jaddada cewa yana da dukkanin abin da ake buƙata domin riƙe kujera mafi girma ta mulki a ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng