"PDP ba Ta da Masaniya," Gwamna Makinde Ya Hango Kuskuren Atiku a Shirin Haɗakar 2027
- Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa PDP ba ta da masaniya kan shirin haɗakar ƴan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta
- Makinde ya ce ba zai yiwu a ƙulla kawance da 'yan adawa ba tare da sanar da shugabannin PDP ba kuma a sanya jam'iyyar a ciki
- Gwamnan ya ce gwamnonin PDP sun yi fatali da haɗakar ne bayan tattaunawa da shugagannin jam'iyya a taron da suka yi a Ibadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa babu wani tsarin hadin gwiwa, kawance ko dunkulewa da jam’iyyar adawa ta PDP ke da masaniya a kai.
Gwamna Makinde ya ce PDP ba ta san komai ba dangane da haɗakar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta da nufin kifar da gwamnatin APC a 2027.

Asali: Facebook
Seyi Makinde ya yi wannan furucin ne a hirar da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde ya yi fatali da haɗakar Atiku
A cewarsa, irin wannan yunkuri dole ne ya kasance bisa tsarin jam'iyyar PDP kuma a sanar da ita komai tare da cikakken bayani kan yunkurin kafin ta ɗauki mataki.
"Ba zai yiwu mu wayi gari da safe wani ɗan jam'iyya ya ce ya sanya jam'iyyarmu cikin haɗaka ba tare da masaniyar shugabanni ba, ba su san komai kan shirin ba.
"Ba su san abin da ke cikin wannan kawance ba. Ba su san ko wani yunkuri ne na kashin kai ko kuma wani abu ne da ke da amfani ga jam’iyya da Najeriya gaba daya ba.
- Seyi Makinde.
Atiku da wasu jiga-jigai da suka hada da Malam Nasir El-Rufai sun sanar da kafa haɗaka domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.

Kara karanta wannan
'Mun ba ka zaɓi': PDP ta taso gwamna a gaba, ta buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
Makinde na tare da matsayar gwamnonin PDP
Sai dai Makinde ya jaddada matsayar Gwamnonin PDP, inda suka nesanta kansu daga wannan haɗaka.
Ya ce gwamnoni sun yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP, rahoton The Nation.
Ya kara da cewa shugabannin PDP na kasa ciki har da mukaddashin shugaban jam’iyya, Umar Damagum sun halarci taron gwamnoni a Ibadan.

Asali: Twitter
A cewar Makinde:
"Dole sai da tsari kafin jam’iyya ta shiga kowanne irin kawance ko hadaka. Idan wasu mutane ne suka yanke shawarar a kashin kansu, suna da ‘yancin hakan.
"Amma a wurin jam’iyyar PDP, har yanzu ba mu kai ga wannan mataki ba. Babban aikinmu yanzu shi ne mu gyara jam’iyya mu sanya ta a kan turba mai karfi."
Makinde ya yi maganar takarar 2027
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce zaben 2027 mai zuwa zai gudana ne tsakanin jam'iyyar APC da ƴan Najeriya.
Gwamna Makinde ya dora laifin tabarbarewar tattalin arziki da ƙara lalacewa tsaro a ƙasar nan a kan gwamnatin APC.
Bisa haka gwamnan wanda alamu ke nuna yana son neman takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce wuƙa da nama na hannun ƴan Najeriya, su za su yanke hukunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng