2027: Ganduje Ya Sha Alwashin Kwatowa APC Abuja daga Hannun 'Yan Adawa
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce babban birnin tarayya Abuja yana da muhimmancin da ya wuce a bar shi a hannun jam’iyyun adawa
- Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne a wurin taron sauya sheƙa na wasu shugabanni da mambobin jam'iyyun PDP da LP zuwa APC a Abuja
- Ganduje ya ce nasarorin da APC ke samu a Abuja sun sa jama’ar Abuja ke kara amincewa da jam’iyyar gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce birnin tarayya Abuja na da matsayi na musamman a Najeriya, don haka ba za a bar shi a hannun 'yan adawa ba.
Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a wani taron sauya sheƙa da aka gudanar a wani filin taro a Abuja, inda wasu ‘yan jam’iyyar PDP da LP suka sauya sheƙa zuwa APC.

Asali: Facebook
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan 'yan APC da wasu jami'an gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka sauya sheƙar sun hada da shugaban karamar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC), Chris Maikalangu, wanda ya jagoranci tawagar.
'Ba za a bar wa 'yan adawa Abuja ba,' Ganduje
Ganduje ya ce sauya shekar ya nuna yadda jama’ar Abuja ke kara fahimtar nasarorin gwamnatin APC, yana mai cewa hakan na nuna yuwuwar samun nasarar sake zaben Bola Tinubu a 2027.
Punch ta wallafa cewa ya ce kasancewar Abuja ita ce cibiyar mulki da haduwar al’ummar Najeriya, bai kamata jam’iyyun adawa su rike ta ba.
A cewar Abdullahi Ganduje, dole ne a tabbatar da cewa APC ce ke da rinjaye a matakan shugabanci na birnin.
A halin yanzu, Sanata mai wakiltar Abuja, Ireti Kingibe da wani dan majalisar wakilai, Joshua Obika, duk ‘yan jam’iyyar LP ne, yayin da Abdulrahman Ajiya ne dan APC.
Minista ya yaba wa Bola Tinubu
Zephaniah Jisalo, wanda dan asalin Abuja ne, ya jinjinawa Shugaba Tinubu bisa cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen, musamman wajen bai wa ‘yan Abuja mukamai.
Ya ce Tinubu ya nuna kulawa ta musamman ga al’ummar yankin, wanda hakan ya kara jawo wa APC karbuwa a Abuja da sauran sassan ƙasa.
An bukaci kara goyon bayan APC a Abuja
Karamar ministar Abuja, Mariya Bunkure ta bukaci jama’ar FCT da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin APC, tana mai cewa gwamnati na aiki tukuru wajen inganta rayuwar su.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, shugabannin kananan hukumomi da sauransu.

Asali: Twitter
Sanata Ubale Shitu ya koma SDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Jigawa, Sanata Ubale Shehu ya sauya sheka zuwa SDP.
Sanata Ubale Shitu ya sanar da komawa jam'iyyar SDP ne yayin wani gagarumin taro da aka shirya a Abuja.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da Manjo Hamza Al-Mustapha na cikin wadanda suka tarbe shi a ofishin SDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng