"An Sake Ruguza Ƴan Adawa": Ɗan Majalisa da Wasu Manyan Kusoshi Sun Fice daga PDP

"An Sake Ruguza Ƴan Adawa": Ɗan Majalisa da Wasu Manyan Kusoshi Sun Fice daga PDP

  • Jam'iyyar LP ta ƙara karfi a jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya a lokacin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027
  • Ɗan majalisar dokokin Abia, Hon. Lucky Johnson da wasu manyan kusoshi sun bar PDP tare da komawa jam'iyyar LP mai mulki
  • Gwamna Alex Otti ya yabawa masu sauya shekar bisa matakin da suka ɗauka, yana mai ba su tabbacin cewa ba zai ba su kunya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Zababbun shugabanni da wasu fitattun 'yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a jihar Abia sun sauya sheka zuwa jam’iyyar LP mai mulki a jihar.

Wannan sauya sheka dai ta rage ƙarfin adawa a jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya yayin da aka fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Gwamna Alex Otti.
Dan majalisa da manyan jiga-jigai sun sauya sheƙa zuwa LP a jihar Abia Hoto: Alex C. Otti
Asali: Facebook

Ɗan Majalisa da jiga-jigan siyasa sun koma LP

Vanguard ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai dan majalisar dokokin Abia mai wakiltar Isuikwuato, Lucky Johnson (PDP) da magabacinsa, Chukwudi Ogele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da dan takarar gwamna na jam’iyyar AA a 2023, Onyekwere Akim Uche (OAU), tsohon kwamishinan wasanni, Henry Agbaeze (PDP); da kuma Emma Ibegbulam da wasu da dama.

Dukkan waɗannan kusoshin siyasar sun fice daga jam'iyyunsu, sun koma LP mai mulki a jihar Abia.

Me yasa jiga-jigan suka zaɓi shiga LP?

Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun yanke shawarar barin jam’iyyunsu ne saboda ganin irin kyawawan ayyuka da Gwamna Otti ke aiwatarwa a fadin jihar.

A cewarsu, da farko ba su yarda za a iya gyara Abia da sauri haka ba, amma ganin yadda abubuwa ke tafiya, ya sa suka yanke shawarar marawa Gwamnan Otti baya don ci gaban jihar.

An gudanar da bikin tarbar masu sauya shekar ne a makarantar Isuikwuato High School da ke Otankpa, kuma dandazon mutane daga jam’iyyu daban-daban sun halarta.

Gwamna Abia ya yaba wa masu sauya sheka

A jawabinsa, Gwamna Otti ya yaba da matakin masu sauya shekar, yana mai cewa sun zabi gaskiya kuma sun rungumi haske.

Ya yi alkawarin cewa za a samu karin ci gaba a jihar nan da watanni masu zuwa, yana mai cewa manufarsa ita ce kawo kyakkyawan mulki ga al’umma.

Gwamnan ya kuma godewa al’ummar jihar Abia bisa goyon bayan da suke ba shi, yana tabbatar musu cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen cika alkawuran da ya ɗauka.

Jam'iyyar LP.
LP ta kara karfi a jihar Abia Hoto: Labour NG
Asali: UGC

Otti ya kamo hanyar gyara wutar lantarki

Game da batun wutar lantarki, Gwamna Otti ya ce tuni ya amince da gina tashar wutar lantarki mai zaman kanta a jami’ar jihar watau ABSU.

A cewarsa, hakan na daga cikin shirin da yake na sake gyara jami’ar da kuma warware matsalar rashin wuta a yankin gaba daya.

A cewarsa:

“Cikin gyaran da ake yi a jami’ar jihar Abia, na amince da gina wata tasha mai zaman kanta da za ta samar da lantarki har megawat 10."

Gwamna Otti zai nemi kujerar sanata?

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Abia, Alex Otti ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa zai nemi kujerar sanata bayan ya kammala wa'adi na biyu.

Otti ya ce jita-jitar da ake yaɗawa ba gaskiya ba ce kuma bai taɓa tunanin tafiya Majalisar Dattawa ba bayan ya sauka daga mulki.

Haka kuma, Otti ya bayyana shirin gwamnati na sake duba batun korar ma’aikata 154 da aka yi a 2011, waɗanda galibinsu malaman makaranta ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262