'Jama'a Sun Gamsu da Mulkin APC,' Barau Ya Yi Hasashen Abin da zai Faru a Zabe
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa akwai alamun jama'a sun amince da salon mulkin Bola Tinubu
- Sanata Barau ya bayyana hakan ne yayin da manyan APC suka tarbi shugaban karamar hukumar birnin Abuja, Christopher Maikalangu
- Ya ce yawan sauya sheka zuwa jam'iyyu da ake samu a 'yan kwanakin nan na nuna cewa APC ce za ta yi nasara a zaɓuka masu zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a duka zabukan da za a gudanar nan gaba a Abuja.
Sanata Barau ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis yayin taron haɗin kan jam’iyyar da aka gudanar a tsohon filin fareti da ke Area 10, Abuja.

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya ce an shirya taron domin tarbar shugaban karamar hukumar birnin Abuja, Christopher Maikalangu, da masoyansa zwa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci sauran 'yan kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar wajen tarbar sabbin mambobin da suka sauya sheƙa.
Jama’a sun aminta da APC – Barau Jibrin
Jaridar The Cable ta ruwaito Barau yana cewa yawan 'yan adawa da ke shiga jam’iyyar APC na nuna irin kwarin gwiwar da 'yan Najeriya ke samu kan shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce:
“Wannan wani babban taro ne mai matuƙar muhimmanci, domin jirgin APC da na shugaban jam’iyya na ƙasa yana yawo a faɗin ƙasar nan yana tarbar dubban mutane zuwa jam’iyyarmu mai albarka.”
“Yau kuma ya sauka a babban birnin tarayya, Abuja. Shugaban jam’iyya na ƙasa da sauran 'yan NWC suna aiki tukuru wajen jawo mutane zuwa APC. A ‘yan kwanakin nan dubban mutane sun shiga jam’iyyar.”

Asali: Facebook
Ya bayyana sauya shekar Maikalangu da magoya bayansa a matsayin babban nasarar siyasa ga APC a babban birnin tarayya.
Barau: 'APC za ta karɓi Abuja gaba ɗaya'
Sanata Barau Jibrin, ya ce taron wata alama ce ta gagarumar nasara, domin Maikalangu, na da muhimmanci da tarin magoya baya a yankinsa.
Barau ya ce:
“Wannan zai sauya tsarin siyasa a Abuja. Da ikon Allah, za mu lashe zaɓuɓɓuka da gagarumin rinjaye duk lokacin da aka gudanar da su.”
Ya kuma yi kira ga 'yan am’iyyar da su haɗa kai domin tallafa wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Ya ƙara da cewa:
“Mun sha faɗi cewa kafin zuwan Shugaban ƙasa Tinubu, ƙasar nan na fuskantar matsaloli daban-daban – daga bangaren ababen more rayuwa, tsaro, makamashi da sauransu.”
“Ya zo da niyyar sauya labarin. Amma rikice-rikicen duniya kamar na Rasha da Ukraine da na Isra’ila da Falasɗinu sun kawo tashin farashin kaya da ayyuka a duniya. Tabbas, Najeriya ba za ta tsira ba.”
Barau ya ce duk da ƙalubalen duniya, Shugaba Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen gina Najeriya.
An karyata shirin komawar Kwankwaso APC
A wani labarin kuma, Fitaccen jigon NNPP, Buba Galadima, ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Injiniya Buba ya ce babu gaskiya a batun da wasu ke yadawa cewa Kwankwaso zai sauya sheka zuwa APC, yana mai zargin APC da magana a kan zabe tun kafin mulki ya yi nisa.
Ya ce NNPP na ci gaba da jan hankalin ’yan Najeriya da irin nagarta da akidu da take da su, tare da nuna wa yan Najeriya za su yi mulki na gaskiya da rikon amana idan aka ba da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng