Matashin da Hisbah Ta Kama a Kano Ya Fadi Babban Dalilin Aikata Baɗala da Akuya
- Jami'an hukumar Hisbah a Kano sun cafke wani matashi bayan an gan shi a wani bidiyo yana wani abu da akuya da ake zargi da baɗala
- Matashin, mai suna Shamsu Yakubu daga Dawakin Tofa, ya bayyana cewa ya aikata hakan ne domin ya shahara a dandalin TikTok
- Sai dai a lokacin da jami’an Hisbah suka tsare shi, ya rantse da Allah SWT cewa bai tsotsi jikin akuyar ba, sai dai ya kai bakinsa kusa ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dawakin-Tofa, Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wani matashi bisa zargin aikata baɗala da akuya.
Hukumar ta cafke matashin ne bayan wani bidiyo ya yadu a shafukan sada zumunta na zamani.

Asali: Original
Hisbah ta kama matashin kan zargin baɗala
An bayyana cewa matashin mai suna Shamsu Yakubu, ɗan shekaru 24 ya fito ne daga karamar hukumar Dawakin Tofa, Aminiya ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya bayyana a cikin faifan bidiyon yana tsotsar farjin akuya a dandalin TikTok.
Yaron ya ce:
“Na rantse da Allah ban tsotsi Akuyar ba, bakina kawai na kai kusa da wurin."
Da yake mayar da martani kan lamarin, Mataimakin Kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Mujahidden Aminuddeen Abubakar, ya bayyana matakin da Shamsu ya ɗauka a matsayin abin kunya.
Ya ce abin da ya yi babban abin ƙyama ne da ya ci karo da koyarwar addinin Musulunci da kuma ɗabi’un kirki.
Ya ce:
"Abun takaici ne yadda mutum ɗan Musulmi zai jefa kansa cikin irin wannan aikin ban kunya, yana watsi da duk wata daraja ta addini da ɗabi’a.
"Wannan mutum ya nuna rashin fahimtar Musulunci kwata-kwata. Yunkurinsa na neman ɗaukaka a soshiyal midiya ba tare da kishin mutunci ba ne ya jefa shi cikin wannan tozarci."

Asali: Facebook
Umarnin hukumar Hisbah kan matashin a Kano
Hukumar Hisbah ta sake jaddada aniyarta na kare ɗabi’a da tarbiyya, tare da gargaɗi ga duk masu ƙoƙarin lalata tsarin al’adun da addinin jihar.
Halayyar ban mamaki da matashin ya nuna ta fusata al’umma sosai, har wasu daga cikinsu suka yi barazanar ɗaukar doka a hannunsu, cewar Leadership.
Wanda ake zargin ya ƙara bayyana cewa bai yi amfani da miyagun ƙwayoyi ko kayan maye ba a lokacin da lamarin ya faru.
Sai dai hukumar Hisbah ta bayar da umarnin gudanar da cikakken gwajin kwakwalwa da kuma na amfani da kwayoyi domin tantance halin da yake ciki.
An kai wa yan Hisbah hari a Katsina
Kun ji cewa ‘yan sanda a Katsina ta cafke Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu su uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, har suka jikkata su.
Hisbah ta ce jami’anta sun je dakatar da matasa daga wasan ƙwallo kusa da masallaci, amma sai matasan suka kore su.
A lokacin arangamar, Alhaji Surajo Mai Asharalle ya harba bindiga sau da yawa, inda ya jikkata jami’an Hisbah biyar da ke bakin aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng