Yadda aka Kuskure Natasha wajen kai Hari Gidansu da Agajin da 'Yan Gari Suka kai
- An kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke Obeiba-Ihima, Kogi yayin da dan uwanta ke rangadin duba kwangiloli
- Natasha ta bayyana cewa harin na da alaka da siyasa, inda ta bukaci sufeton ‘yan sanda ya dawo da jami’an tsaronta da aka janye mata
- Ta zargi shugaban majalisar dattawa, tsohon gwamna Yahaya Bello da Gwamna Usman Ododo da hannu idan wani abu ya same ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci rundunar ‘yan sanda da ta dawo da jami’an tsaronta da aka janye tun watan Maris.
A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaranta ya fitar, Natasha ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari gidan iyayenta da ke Obeiba-Ihima a jihar Kogi.

Asali: Twitter
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, Natasha ta fadi wadanda za a kama idan wani abu ya same ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuskure Natasha yayin ziyarar dan uwanta
Jaridar Punch ta wallafa cewa Natasha Akpoti ta ce an kai harin ne a lokacin da dan uwanta ya je duba wasu ayyuka.
Sanatar ta bayyana cewa lamarin na da nasaba da siyasa, tana mai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne bisa tunanin cewa ita ce take cikin gidan a lokacin.
An kori masu kai hari gidansu Natasha
Natasha ta ce harin ya faru ne a ranar Talata da dare, kuma ya haifar da barna a cikin gidan da ta ce mallakin kakanta ne tun da jimawa.
Sai dai ta ce jami’an tsaron NSCDC da wasu al’ummar gari sun gaggauta kawo dauki, suka fatattaki wadanda suka kawo harin kafin a samu wani rauni ko asarar rai.
Ta yi kira ga sufeton ‘yan sanda da ya gaggauta dawo da jami’an tsaronta da aka janye tun ranar 6 ga Maris bayan wani sabani da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Natasha Akpoti ta bukaci a zauna lafiya
Natasha ta bukaci al’umma da su ci gaba da kwanciyar hankali tare da nuna goyon baya wajen ganin an yi adalci a kan lamarin.
Ta ce rashin tsaro da barazana ba su kamata su zama hanyar dakile ayyukan da take yi wa al’ummarta ba.
Sanata Natasha ta jaddada kudirinta na ci gaba da wakiltar mazabarta da gaskiya da rikon amana.

Asali: Twitter
Wa za a kama kan kai hari a gidan Natasha?
Natasha ta ce idan wani abu ya same ta, to shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, tsohon gwamna Yahaya Bello da kuma Gwamna Usman Ododo ne ke da alhakin hakan.
Sanatar ta bayyana damuwarta kan yadda lamarin tsaro ke kara ta’azzara a jihar, tana mai cewa lokaci ya yi da za a daina amfani da siyasa wajen cutar da jama’a.
Yahaya Bello ya kai karar Sanata Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya karyata zargin cewa zai hallaka Natasha Akpoti.
Yahaya Bello ya bukaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta dauki mataki kan zargin da Natasha ta masa kan kashe ta.
A kwanakin baya ne Sanata Natasha Akpoti ta zargi Yahaya Bello da wasu 'yan siyasa da kokarin halaka ta saboda lamuran siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng