Ibok Ete Ibas: Abubabuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani game da Shugaban Rikon Kwarya a Rivers

Ibok Ete Ibas: Abubabuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani game da Shugaban Rikon Kwarya a Rivers

Bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaba na rikon kwarya a jihar Rivers.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wannan matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa, musamman duba da irin rawar da Ibas ya taka a fannin tsaro da diflomasiyya.

Abubuwa masu muhimmanci game da shugaban rikon kwarya a Rivers
Abubabuwa 6 da ya kamata ku sani kan shugaban rikon kwarya a Rivers, Ibok-Ete Ibas. Hoto: Aso Rock Villa.
Asali: Facebook

Muhimman abubuwa game da Ibok-Ete Ibas

Hakan ya biyo bayan rikice-rikicen siyasa da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar tun bayan zaben 2023 da Siminalayi Fubara ya hau mulki, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta duba muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da shi.

1. Mahaifa da karatu a rayuwar Ibok-Ete Ibas

An haifi Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a ranar 27 ga Satumbar 1960, a garin Nko da ke jihar Cross River.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'laifin' Wike

Ya girma a yankin Kudu kudu maso Kudu na Najeriya, wanda ke da tsatson ruwa da harkokin kasuwanci na teku.

Ya yi karatun firamare da sakandare a jiharsa kafin ya wuce makarantar soja a shekarar 1979, ya shiga Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA), inda ya samu horon soja.

Bayan kammala horon soja, ya shiga rundunar sojan ruwa ta Najeriya a matsayin 'Sub-lieutenant'.

Ya samu digiri na biyu a fannin tsaro da dabarun yaki (Defence and Strategic Studies).

An nada sabon gwamnan rikon kwarya a Rivers
Bola Tinubu ya nada Vice Admiral Ibokette Ibas domin jagorantar jihar Rivers. Hoto: Kemi Talks.
Asali: Facebook

2. Rayuwar Iyali da abin da yake sha'awa

Vice Admiral Ibas yana auren Barista Theresa Ibas, kuma suna da yara da dama da suka haifa.

Bisa al'adar bariki, matarsa ta taɓa zama shugabar NOWA, wata kungiya da ke taimakawa iyalan sojojin ruwa.

A gefe guda, Ibas na da sha’awar karatu, wasan golf, da kallon fina-finan tarihi.

Hakan na nuna cewa shi mutum ne mai son ilimi da bincike, wanda zai iya tasiri a yadda zai tafiyar da jihar Rivers a matsayinsa na shugaban wucin gadi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

3. Shiga aiki da matsayi a sojan ruwa

A shekara ta 1983, aka naɗa Ibas a matsayin 'Sub-lieutenant' a Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, cewar The Guardian.

A tsawon shekarun hidimarsa, ya rike mukamai da dama, ciki har da: shugaban gudanarwa a hedikwatar hukumar sojojin ruwa (2011-2012) da jami'i mai kula da tuta a hedikwatar 'Western Naval Command' (2013-2014).

Sai kuma Jami'i mai kula da sashen kayayyaki a shekarar 2014 da muƙamin Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa na Najeriya (2015-2021).

A matsayinsa na Babban Hafsan Sojan Ruwa, Ibas ya jagoranci yaki da fasa kwauri da satar danyen mai a Najeriya.

4. Manyan ayyukansa da nasarori

A tsawon lokacin da ya yi a matsayin shugaban rundunar sojan ruwa, Ibas ya kaddamar da sababbin shirye-shirye don inganta tsaro a bakin teku.

Ya jagoranci shirin "Deep Blue Project," wanda ke da nufin kawo karshen 'yan fashin teku da miyagun laifuffuka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

Hafsun ya inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasashen ketare wajen tsaron ruwa, ciki har da kasashen Gulf of Guinea.

Sannan ya tabbatar da samar da sabbin jiragen ruwa na yaki da kuma amfani da fasahar zamani don kara karfin sojan ruwa.

Wadannan nasarori sun jawo masa yabo daga masu ruwa da tsaki a fannin tsaro a Najeriya da ma kasashen waje.

Tinubu ya dakatar da gwamna Fubara a Rivers
Bola Tinubu ya dakatar da gwamnatin Rivers na tsawon watanni 6. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: UGC

5. Ayyukan da ya yi bayan ritaya

Bayan ya yi ritaya daga rundunar sojan ruwa a shekarar 2021, an naɗa shi a matsayin Jakadan Najeriya a Ghana.

A wannan matsayi, ya wakilci Najeriya a taruka na diflomasiyya, ya taimaka wajen inganta dangantakar Najeriya da Ghana, da ma sauran kasashen yammacin Afirka.

Naɗinsa a matsayin jakada ya nuna cewa ya na da kwarewa ba kawai a fannin soja ba, har ma a harkokin siyasa da diflomasiyya.

6. Naɗinsa a matsayin shugaban rikon kwarya

Bayan rikicin siyasa da ya kunno kai a Jihar Rivers, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ibas a matsayin shugaba na rikon kwarya.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

Channels TV ta ce wannan na da alaka da kwarewarsa a fannin tsaro da iya magance rikice-rikice da rashin bangaranci a cikin siyasar jihar da sha’anin mulki da diflomasiyyar da ya koya.

Tinubu ya nada gwamnan rikon kwarya a Rivers
Bayan rikice-rikicen siyasa a Rivers, Bola Tinubu ya nada gwamnan rikon kwarya. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Dokar ta ɓaci: APC ta gargadi jihar Osun

Kun ji cewa Jam’iyyar APC ta goyi bayan matakin sanya dokar ta-ɓaci a Rivers, tana mai cewa saura gwamnan Osun, Ademola Adeleke idan bai mayar da hankali ba.

Rahotanni sun nuna cewa an fara neman jefa Adeleke a matsala bayan dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng