Dakatar da Fubara: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan 'Laifin' Wike
- Rahotanni na nuni da cewa Antoni Janar na Tarayya ya ce ba laifin Nyesom Wike ba ne ya jawo ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers
- Lateef Fagbemi ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ne ya haddasa rikicin ta hanyar rusa Majalisar Dokokin Jihar da sauran abubuwa
- Baya ga haka, Lateef Fagbemi ya bukaci masu adawa da matakin da Bola Tinubu ya dauka su kai kukansu gaban Majalisar Tarayya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ba shi da hannu a rikicin da ya kai ga ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.
A ranar Talata ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar mai arzikin mai, yana mai cewa matsalar siyasa ce ta haddasa hakan.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi SAN ya bayyana haka ne a yau Laraba yayin hira da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar jihar na tsawon watanni shida, tare da nada tsohon hafsan sojan ruwa, Ibok Ibas, a matsayin mai rikon kwarya.
Nyesom Wike ya kubuta daga zargi?
Duk da haka, mutane da dama sun zargi Shugaba Tinubu da nuna fifiko ga Wike, wanda ake zargi da haddasa rikicin siyasar jihar.
A yayin wata hira da gidan talabijin na Arise, fitaccen dan jarida, Mahmud Jega, ya ce ya kamata a dora wa Wike alhakin rikicin, kasancewarsa jigon rabuwar kai a majalisar dokokin jihar.
Jega ya ce:
“Shugaban kasa ya bayyana laifuffukan Fubara, amma bai ce komai kan Ministan FCT ba, wanda ke da hannu a wannan rikici.”
Ya kara da cewa Wike yana amfani da tasirinsa daga Abuja wajen kawo matsala a jihar da ya taba mulka, kuma idan ba a dauki matakin da ya dace ba, za a ci gaba da fama da matsalar har 2027.
Gwamnatin tarayya ta dora laifi kan Fubara
A martaninsa yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, Antoni Janar ya dora alhakin rikicin siyasar Rivers kan Gwamna Fubara.
Ya ce Fubara ne ya haddasa matsalar ta hanyar rusa ginin majalisar dokokin jihar da nufin hana yunkurin tsige shi daga mukaminsa.
Fagbemi ya ce:
“Lokacin da batun kasa ya taso, dole ne a fadi gaskiya. Shin Wike ne ya umarci a rushe Majalisar Dokokin Jihar Rivers? Ba hannun Ministan FCT a wannan batu.”
Ya kara da cewa Kotun Koli ta tabbatar da cewa Gwamna Fubara ne ya haddasa matsalar ta hanyar daukar matakin da ba bisa doka ba.
Ya ce idan har Kotun Koli ta ce babu gwamnati a jihar, to Shugaban Kasa bai da wani zabin da ya wuce daukar matakin da ya dace don tabbatar da doka da oda.
Rawar da majalisa za ta taka kan lamarin
Fagbemi ya shawarci masu adawa da dokar ta-baci su kai kukansu ga Majalisar Tarayya, domin ita ce ke da ikon tabbatar da matakin ko soke shi.
Ministan shari'ar ya ce:
“Idan Majalisar Tarayya ta ga cewa matakin Shugaban Kasa bai dace ba, ba za ta amince da shi ba.”

Asali: Facebook
'Yan Neja Delta sun yi magana kan Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen yankin Neja Delta sun gargadi shugaban kasa Bola Tinubu kan sanya dokar ta baci a jihar Rivers.
Mutanen yankin sun ce suna jin tsoro kar masu tayar da kayar baya su yi amfani da damar wajen cigaba da fasa bututun mai a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng