"Duk Shiri ne," Babachir Lawal Ya Sake Tabo Yadda ADC Ta Tsaida Atiku Takarar Shugaban Kasa
- Ana ci gaba da musayar yawu tsakanin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar
- Bayan zarge-zargen da ya yi a baya, Babachir Lawal ya suki Atiku kan yadda ya samu tikitin takarar ADC ba tare da ya sha wahala ba
- Ya kuma nanata cewa ya fice daga ADC ne bayan zaben fidda gwani, yana mai zargin cewa an samu kura-kurai da dama a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir David Lawal, ya sake caccakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Atiku Abubakar.
Babachir ya yi ikirarin cewa Atiku bai bai sha wahala ba wajen neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, yana mai cewa cikin sauki ya zama dan takara a 2027.

Source: Twitter
Babachir Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, 226 yayin wata hira da ya yi da tashar Channels TV a shirin Politics Today.
Wannan kalamai na sa na zuwa ne kwanaki kadan bayan ya fice daga jam’iyyar ADC saboda zaben fidda gwani da ya ce akwai kura-kurai a cikinsa.
Babachir ya yaba da kokarin Amaechi
Tsohon SGF ya ce ya yi tsammanin fafatawa mai tsanani tsakanin manyan ‘yan takara, musamman ganin yadda tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ya nuna himma sosai.
“Mutum irin Rotimi Amaechi yana da cikakken yakini cewa idan aka je zaben fidda gwani zai yi nasara. Duk wadanda ke tare da shi suna da irin wannan tabbaci,” in ji Lawal.»
Ya kara da cewa Amaechi na daga cikin ‘yan takarar da ke zagayawa suna neman goyon baya da kuma yin aiki tukuru domin samun tikitin jam’iyyar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Babachir Lawal ya kara tabo Atiku
Babachir Lawal ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar bai sha wata wahala wurin yakin neman tikitin ADC, yana mai cewa hakan ya nuna shiri aka yi tun farko.
“Sai kuma Atiku Abubakar. A wancan lokacin muna tambayar kanmu me zai yi domin ya lashe zaben fidda gwani, domin bai yi wani abu sosai ba, bai fita kamfe ba, bai yi magana sosai ba, bai zagaya wurraren mambinin jam'iyya ba,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya ce wannan ne ya sa su ke cikin rudani kan yadda Atiku ya iya samun tikitin takarar ADC duk da bai yi wani abin a zo a gani, wanda zai nuna ya cancanci samun nasara ba.
Babachir ya kuma nanata cewa ya fice daga ADC ne bayan zaben fidda gwani, yana mai zargin cewa an samu kura-kurai a tsarin zaben da kuma cewa Atiku ya yi amfani da karfi wajen samun nasara.
Atiku ya caccaki Babachir Lawal
A baya, kun ji cewa Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir lawal.
Atiku ya zargi Babachir da yin kalamai da ka iya rusa hadin kan da ke tsakanin 'yan Najeriya da kuma nuna bambancin kabila.
Atiku ya ce abin takaici ne yadda Babachir ya zabi yin zarge-zarge dahasashe ba tare da gabatar da hujjojin da za su gaskata maganganunsa ba.
Asali: Legit.ng


