Bayan Fubara, APC Ta Yi Barazanar Dakatarwa ga Gwamnan PDP a Osun

Bayan Fubara, APC Ta Yi Barazanar Dakatarwa ga Gwamnan PDP a Osun

  • A ranar Talata shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta-baci a jihar Rivers saboda rikicin siyasa da kuma barazanar tsaro
  • Jam’iyyar APC ta goyi bayan matakin, tana mai cewa zai dawo da doka da oda a Ribas, kuma ta gargadi gwamnan Osun
  • Bayanai sun nuna cewa an dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki na tsawon watanni shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta nuna goyon bayanta ga matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa a ranar Talata, yana mai cewa rikicin siyasa da matsalolin tsaro sun tilasta masa daukar matakin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Rivers ta fadi mamakin da Tinubu ya ba ta kan dakatar da Fubara

Fubara
APC ta goyi bayan Tinubu kan dakatar da Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Wike|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an nada tsohon hafsan sojin ruwa, Ibok-Ete Ibas, a matsayin sabon mai kula da jihar yayin dokar ta-bacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ayyana dokar ta-baci a Rivers

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an samu rahotannin tsaro masu tayar da hankali a jihar Rivers, ciki har da ayyukan ‘yan bindiga da lalata bututun mai.

Ya ce babu kokari daga bangaren gwamnati wajen shawo kan matsalar, lamarin da ya zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban jihar.

Tinubu ya kara da cewa rikicin siyasa da rashin jituwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ya hana jihar samun ci gaba.

A saboda haka ne aka dauki matakin dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa watau Ngozi Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Jam'iyyar APC ta goyi bayan matakin Tinubu

Sakataren jam’iyyar APC, Ajibola Basiru, ya bayyana cewa matakin Shugaba Tinubu abu ne mai kyau wanda zai dawo da doka da oda a Rivers.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya ta kare matakin sauke gwamnatin Ribas na watanni 6

Ya ce jihar Rivers na fuskantar barazanar zama jiha da ta gaza, don haka ya kamata a dauki matakin da zai tabbatar da tsaro da ci gaba.

Basiru ya kuma caccaki gwamnati da majalisar dokokin Rivers, y ana mai cewa sun gaza wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya daura masu.

APC ta gargadi gwamnan Osun

Ajibola Basiru ya bukaci gwamnan Osun da ya dauki darasi daga wannan lamari ta hanyar barin shugabannin kananan hukumomi da kotu ta mayar su ci gaba da aiki.

Jaridar The Sun ta wallafa cewa Basiru ya ce idan gwamnan bai dauki darasi ba, zai iya fuskantar hukunci irin na jihar Rivers.

Gwamnan Rivers
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Sabon mai kula da jihar Rivers

Bayan ayyana dokar ta-baci, shugaba Tinubu ya nada tsohon hafsan sojin ruwa, Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da jihar Rivers.

Ya ce sabon mai kula da jihar zai yi aiki ne domin kare muradun al’umma da tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Ka nesanta kan ka da Rivers': PDP ta gargaɗi 'shugaban riƙo' da Tinubu ya nada

Sai dai dokar ta-bacin ba ta shafi bangaren shari’a ba, domin kotuna za su ci gaba da gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.

Fubara ya yi jawabi bayan dakatar da shi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara ya yi jawabi ga jama'arsa.

Gwamna Fubara ya umarci mutanen jihar Rivers su cigaba da bin doka da oda, inda ya ce dama mutanen jihar sun saba jajircewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng