Rikicin Rivers: Manyan Zunubai 3 da Tinubu Ya Nuna Gwamna Fubara Ya Aikata
- Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin Rivers bayan rikicin siyasa da ya addabi jihar
- A jawabin da ya gabatar ga al’umma a daren ranar Talata, 18 ga Maris, Tinubu ya bayyana cewa sau uku Gwamna Fubara yana yi wa doka hawan ƙawara
- Shugaban ƙasa ya kuma tuna cewa ya yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, amma bangarorin da abin ya shafa sun ƙi bin hanyoyin warware rikicin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - A ranar Talata, 18 ga watan Maris, shugaba Bola Tinubu ya ya ayyana dokar ta ɓaci a Rivers, bayan gaza cimma maslaha tsakanin bangarorin siyasar jihar.
Hakan ya biyo bayan rikicin siyasa da aka daɗe ana yi tsakanin manyan ƴan siyasa biyu a jihar, Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon gwamnan jihar kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Asali: Facebook
Bola Tinubu ya sa dokar ta ɓaci a Rivers
Hadimin shugaban ƙasa kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ya sanya jawabin shugaban ƙasan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasan ya kuma dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar har na tsawon wata shida.
Yayin da yake bayyana dakatarwar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana ƙoƙarinsa na dawo da zaman lafiya a jihar, da kuma gazawar ɓangarorin siyasar wajen kawo maslaha.
Laifukan Gwamna Fubara a idanun Tinubu
Shugaban ƙasan ya bayyana abubuwa guda uku da Gwamna Fubara ya yi, waɗanda suka nuna ya karya doka.
Abubuwan sun haɗa da:
1. Rushe ginin majalisar dokoki
Tinubu ya bayyana cewa Gwamna Simi Fubara ya rushe ginin majalisar dokokin jihar a ranar 13 ga watan Disamba, 2023, ba tare da wani dalili mai inganci ba.
Jawabin shugaban kasar ya kuma koka da cewa bayan watanni 14 da wannan abin takaici, gwamnatin Ribas ba ta sake gina shi ba.
2. Rashin aiwatar da hukuncin Kotun Koli
Shugaba Tinubu ya kuma ce Gwamna Fubara ya ƙi aiwatar da hukuncin Kotun Koli, musamman kan sake gabatar da kasafin kuɗin jihar.
Mai girma Tinubu ya ce gwamnan da ƴan majalisar suna buƙatar yin aiki tare don tabbatar da cigaban dimokuraɗiyya.
Ya ambaci wani ɓangare na hukuncin Kotun Koli da ke cewa Gwamna Fubara da gangan ya rushe majalisar dokoki domin yin mulki ba tare da wani ƙuntatawa ba, wanda hakan ke nufin “a halin yanzu babu gwamnati a jihar Rivers.”
3. Rashin yin Allah wadai da barazanar matasan Ijaw
Tinubu ya kuma ce wasu tsageru sun yi barazana ga waɗanda suke ganin abokan gaba ne ga gwamnan, amma Fubara bai nisanta kansa daga barazanar ba har sai da aka ayyana dokar ta-baci a ranar Talata, 18 ga watan Maris.
A ranar Laraba, 5 ga watan Maris, ƙungiyar matasan Ijaw (IYC) ta yi barazanar hana haƙo mai a yankin Neja Delta idan majalisar dokokin Rivers ta tsige Gwamna Fubara bisa hukuncin Kotun Koli.
Tinubu ya bayyana cewa rahoton tsaro ya nuna cewa a ranar Litinin da Talata, tsageru sun fara lalata bututun mai a jihar, amma gwamnan bai ɗauki matakin dakatar da su ba.
Tinubu ya naɗa gwamnan riƙo Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa gwamnan riƙo a jihar Rivers, bayan sanya dokar ta ɓaci.
Shugaba Tinubu ya naɗa Air Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai ja akalar gwamnatin rikon ƙwarya a jihar Rivers mai arziƙin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng