Jigon APC A Gombe Ya Musanta Ikirarin Cewa Pantami Ya Yi Murabus Kafin Komawa PDP
- Jam'iyyar APC ta dauko hanyar da ka iya jawo cikas ga takarar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami a zaben gwamnan jihar Gombe
- Shugabannin APC na mazabar Pantami sun ce ba su da masaniyar ficewar Farfesa Isa Ali Pantami daga jam'iyya mai mulki kafin ya koma PDP
- Sun ce ba su karɓi wasiƙar sauya sheka daga tsohon ministan ba, inda suka ce babu wata hujja da aka gabatar masu kafin ya koma PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Jam'iyyar APC ta yi fatali da ikirarin cewa tsohon ministar sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya fita daga jam'iyya mai mulki kafin ya shiga PDP.
Shugabannin jam'iyyar APC na mazabar Pantami da ke Ƙaramar Hukumar Gombe a Jihar Gombe ne suka bayyana hakan, inda suka ce ba su da ssmaniyar Pantami ya bar APC kafin ya koma PDP.

Kara karanta wannan
Tsofaffin shugabannin majalisa da suka yi murabus daga APC kan zaben fitar da gwani

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya ce bayan kasa samun tikitin takarar gwamna a APC, Farfesa Pantami ya koma PDP, inda daga baya ya zama ɗan takarar gwamna na jam'iyyar a zaɓen 2027.
APC ta waiwayi Malam Pantami
A cewar shugabannin APC na mazabar Pantami, babu wata wasiƙa da tsohon ministan ya aike musu domin sanar da su ficewarsa daga APC.
Mataimakin shugaban APC na mazabar Pantami, Yahaya Isa Lawanti, tare da sakataren mazabar, Ibrahim Mohammed Nata, ne suka bayyana haka a taron manema labarai a Gombe.
Sun ce ba su da masaniyar wani murabus da Pantami ya yi daga APC a lokacin da ya zama ɗan takarar gwamna na PDP.
Pantami ya mika takardar barin APC?
Sakataren APC ya ce mambobin kwamitin gudanarwar mazabar Pantami sun samu labarin murabus ɗin ne ta hannun shugaban jam'iyya, Alhaji Bala Galda.
Ya ce shugaban ya sanar da su a wani taro cewa ya karɓi wasiƙar sauya sheka daga tsohon ministan da kansa.
"Ya gaya mana a taro cewa ya karɓi wasiƙar ne a ranar 23 ga Mayu, 2026. Ya kuma ce an rubuta takardar a ranar 19 ga Mayu, 2026, kuma wani mutum mai suna Abba Pantami ne ya kawo ta," in ji shi.
APC na zargin rashin bin ka'ida
Ibarahim Nata ya jaddada cewa duk d sun buƙaci a kawo wasikar su gani amma ba a taɓa gabatar da wasiƙar murabus ɗin Pantmi a gaban kwamitin gudanarwar mazabar ba, wand ya saba ka'ida.
Saboda haka, shugabannin APC sun ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami bai kammala tsarin ficewa daga APC yadda ya kamata ba kafin komawarsa PDP.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Anthony Siyako Yaro mai wakiltar mazabar Gombe ta Kudu ya kai ziyarar girmamawa ga Sheikh Isa Ali Pantami.
Bayan zaman da suka yi, Pantami ya fadi abubuwan da suka tattauna a game da muhimman batutuwan ci gaban al’ummar jihar Gombe.
Sun tattauna kan hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa tare da faɗaɗa damar koyon sana’o’i da samun hanyoyin bunƙasa tattalin arziki a faɗin jihar Gombe.
Asali: Legit.ng
