Tirkashi: Ɗiyar Tsohon Shugaban Najeriya, Obasanjo, Ta Fice daga Jam'iyyar APC
- Sanata Iyabo Obasanjo ta sanar da ficewarta daga APC tana mai zargin shugabannin jam’iyyar da nuna mata rashin mutunci da rashin adalci
- Tsohuwar 'yar majalisar dattawan ta soki tsarin sulhu da ya bai wa Sanata Solomon Adeola tikitin gwamna ba tare da an wani tuntube ta ba
- Iyabo Obasanjo ta kuma yi ikirarin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wajen bayyana dan takarar APC tare da yi musu barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ogun - Tsohuwar sanatar Ogun ta tsakiya kuma ‘yar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Farfesa Iyabo Obasanjo, ta yi murabus daga jam’iyyar APC.
Iyabo ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda abin da ta kira ci gaba da nuna mata rashin mutunci, kin amincewa da gudummawarta da kuma rashin adalci daga shugabannin APC a jihar Ogun.

Source: Twitter
Iyabo Obasanjo ta fice daga APC
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga Mayu 2026, wacce ta aikewa shugaban APC na jihar Ogun, Chief Yemi Sanusi, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar, in ji rahoton Punch.
Iyabo Obasanjo, wacce ke zaune a Amurka inda take koyarwa a matsayin Farfesar fannin ilimin cututtuka, ta soki tsarin sulhu da APC ta yi amfani da shi wajen fitar da Sanata Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, a matsayin dan takarar gwamna.
Ta ce duk da cewa tun farko ta amince za ta mutunta duk wani tsarin sulhu da jam’iyyar ta dauka, ba a tuntube ta ba ko a saka ta cikin tattaunawar kafin a bayyana Adeola a matsayin dan takara.
A cewarta, hakan ya saba wa ka’idojin jam’iyyar APC don haka ta yi sallama da jam'iyyar mai muiki.
An hana magoya bayanta shiga taro

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon
Iyabo ta kuma yi zargin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wajen da aka bayyana dan takarar jam'iyyar APC.
Ta ce wasu daga cikin mabiyanta sun fuskanci barazana da tsoratarwa yayin da ake gudanar da taron bayyana Adeola a matsayin wanda ya lashe tikitin gwamna.
Sai dai duk da rashin jin dadin da ta nuna kan yadda aka gudanar da lamarin, Iyabo ta ce ta amince da hukuncin jam’iyyar ne saboda hadin kai.

Source: Twitter
Tarihin dawowar diyar Obansajo siyasa
Iyabo Obasanjo ta dawo siyasa ne a farkon shekarar nan bayan ta yi rajista a matsayin mambar APC a mazabar 11 da ke Ibogun a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.
A baya ta taba zama kwamishiniyar lafiya ta jihar Ogun tsakanin 2003 zuwa 2007. Haka kuma ta wakilci Ogun ta tsakiya a Majalisar Dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2011.
Bayan ta fadi zaben sake komawa majalisar dattawa a 2011, ta koma kasar Amurka inda ta rage shiga harkokin siyasa har zuwa karshen shekarar 2025.

Kara karanta wannan
An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027
Daga baya ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamnan Ogun karkashin APC kafin daga bisani ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar.
Sanata Iyabo Obasanjo ta gana da Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta gana da Shugaba Tinubu a Lagos inda ta yaba da jagorancinsa.
A lokacin ganawar ta su, Farfesa Iyabo Obasanjo ta jaddada kudirinta na tsayawa takarar gwamnan Ogun a zaben 2027 mai zuwa a jam'iyyar APC.
Ta bayyana cewa tattaunawarsu ta mayar da hankali kan shugabanci, inganta dimokuradiyya da ci gaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
