Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da 'Shugaban Riko' na Jihar Ribas, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabon shugaban riƙo na jihar Ribas, tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya)
- Wannan ganawa ta Mai Girma Tinubu da Ibas na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan shugaban kasa ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas
- Tinubu ya ce ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokoki na tsawon wata shida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa da sabon shugaban riƙo na jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a fadar gwamnati da ke Abuja.
Vice Admiral Ibas mai ritaya, wanda tsohon hafsan rundunar sojan ruwan Najeriya ne, ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin karfe 12:50 na rana domin halartar taron.

Asali: Facebook
Kamar yadda jaridar The Nation ta kawo, wannan taro na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar mai arzikin man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu ya naɗa shugaban riko a Ribas
A daren ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya sanar da nadin Ibas domin jagorantar harkokin mulki a jihar Ribas na rikon ƙwarya.
Shugaba Tinubu ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon rikicin siyasar jihar wanda ke ƙara tsananta a kowace rana, har ta kai ga an fara fasa bututun mai.
Daga cikin matakan da aka dauka, Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan 'yan majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon wata shida a matakin farko.
Wane aiki tsohon hafsan sojin zai yi?
A matsayin sabon jagoran rikon kwarya, Tinubu ya bai wa Vice Admiral Ibas umarnin gudanar da harkokin mulki a jihar, amma ba tare da ikon samar da sabbin dokoki ba.
Sai dai shugaban ƙasa ya jaddada cewa bangaren shari’a zai ci gaba da aiki bisa ‘yanci ba tare da katsalandan ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Dalilin ganawar Tinubu da Vice Admiral Ibas
Ana ganin dai wannan lamari ne ya jawo ganawar shugaban ƙasa da sabon shugaban riko na Ribas yau Laraba yayin da yake shirye-shiryen kama aiki.
Har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton babu wata sanarwa a hukumance kan maƙasudin wannan taro.
Amma ana hasashen taron zai maida hankali ne kan yadda sabon shugaban riƙon zai tafiyar da harkokin jihar Ribas da kuma shawo kan matsalolin da suka haddasa rikici.
Atiku ya martani mai zafi kan batun Ribas
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da matakin ayyana dokar ta ɓace a jihar Ribas.
Atiku ya yi ikirarin cewa duk mai bibiyar harkokin siyasar jihar ya san cewa shugaban kasa Tinubu ke kara rura wutar rikicin ta hanyar goyon bayan ɓangare guda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng