Tinubu Ya Yi Magana bayan APC Ta Yi Barazanar Tsige Gwamnan PDP
- Yayin da rikicin ke kara ruruwa a Ribas, shugaba Bola Tinubu ya bukaci bin doka da oda don dawo da zaman lafiya a jihar
- Shugaban kasar ya ce dole ne a mutunta hukuncin Kotun koli domin tabbatar da dimokuradiyya da ci gaban yankin
- Hakan na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ya yi kamari wanda har ya kai ga barazanar tsige gwamna Simi Fubara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ‘yan siyasa da shugabanni a yankin Kudu maso Kudu su mutunta doka domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Ribas.
Shugaban ya yi wannan kira ne yayin wata ganawa da shugabannin yankin Neja Delta karkashin kungiyar PANDEF a fadar gwamnati da ke Abuja.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Tinubu ya bukaci shugabanni su hada kai domin ceto yankin daga rikicin siyasa da ke barazana ga ci gabansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin ya kara kamari ne yayin da kotu ta ba 'yan majalisar jihar masu biyayya ga Wike nasara kuma wani 'shugaban' APC, Tony Okocha ya yi barazanar tsige Fubara.
Tinubu ya bukaci a mutunta hukuncin kotu
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa dimokuradiyya ba za ta dore ba idan ba a mutunta hukuncin kotu ba, yana mai cewa yana da cikakken kwarin gwiwa ga tsarin shari’a.
Bola Tinubu ya ce:
“Wannan kasa ana tafiyar da ita ne bisa doka. Idan ba tare da doka ba, da ba zan zama shugaban kasa ba. Mutunta kotu wajibi ne a kowane mataki.”
Ya kara da cewa shugabannin yankin su koma gida su tabbatar da an aiwatar da hukuncin kotu a kan lamarin Ribas cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin kungiyar 'Obedient' a Kano, ya ba su shawarwari
“Ina kira gare ku da ku shawo kan gwamna domin a samu zaman lafiya,”
- Bola Tinubu
Tinubu zai kawo cigaba a Neja Delta
A yayin taron, Tinubu ya jaddada cewa yana mai da hankali kan ayyukan ci gaban al’umma, musamman a yankin Neja Delta.
Bola Tinubu ya ce:
“Ci gaban al’umma yana da matukar muhimmanci a gare ni. Shugaban NDDC, Dr Samuel Ogbuku, ya na kokari matuka kuma ya cancanci a kara karfafa shi.”
Shugaban ya kara da cewa ana ci gaba da shirin gina tashoshin jiragen ruwa a jihohin yankin Neja Delta tare da kamfanoni na duniya.

Asali: Facebook
PANDEF ta bukaci karin matakan sulhu
Shugabannin kungiyar PANDEF sun yabawa shugaba Tinubu kan kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da bukatar karin matakai don shawo kan rikicin siyasar Ribas.
Tsohon gwamnan Akwa Ibom, Obong Victor Attah, ya bayyana cewa rikicin siyasar Ribas na barazana ga zaman lafiyar kasa baki daya, don haka yana bukatar kulawa ta musamman.

Kara karanta wannan
El Rufa'i na shirin jan 'yan APC zuwa SDP, Tinubu ya yi magana kan tallafin fetur
Haka zalika, daya daga cikin jagororin PANDEF, King Alfred Diete-Spiff ya gode wa shugaban kasa bisa mukamai da gwamnatinsa ta bai wa ‘yan yankin.
“Gwamnatinka ta dauki matakan gaggawa kan al’amuran da suka shafi yankinmu, kuma muna da kwarin gwiwa cewa za ka samu nasara,”
- King Alfred Diete-Spiff
Tinubu ya yi kira ga gwamnonin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ministoci kan tausayawa talaka.
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira gare su ne yayin liyafar buda baki da ya shirya musu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng