Rikici Ya Ƙara Kamari, Jam'iyyar APC Ta Buƙaci Gwamna Ya Yi Murabus cikin Sa'o'i 48

Rikici Ya Ƙara Kamari, Jam'iyyar APC Ta Buƙaci Gwamna Ya Yi Murabus cikin Sa'o'i 48

  • APC ta ba Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas wa'adin awannni 48 ya yi murabus daga kan kujerarsa cikin lalama da mutunci
  • Shugaban APC na Ribas, Cif Tony Okocha ya yi barazanar cewa idan gwamnan bai yi murabus ba, Majalisar Dokokin jihar za ta tsige shi
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa tsakanin Mai girma Fubara da tsohon uban gidansa, Nyesom Wike ya damalmale

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Ribas ta bukaci Gwamna Siminalayi Fubara ya yi murabus daga muƙaminsa cikin sa’o’i 48.

Jam'iyyar ta kuma yi wa gwamnan barazanar cewa idan har bai yi murabus ba cikin wannan wa'adi, Majalisar Dokokin Jihar za ta tsige shi.

Gwamna Fubara.
APC ta ba Gwamna Fubara wa'adin kwanaki 2 ya yi murabus cikin mutunci Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Shugaban APC na Ribas, Cif Tony Okocha, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a gidansa da ke Fatakwal da safiyar yau Litinin, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin APC ta neman gwamna ya yi murabus

Okocha ya zargi Gwamna Fubara da cin mutuncin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a lokacin da ya yi kokarin samar da mafita ta siyasa dangane da rikicin Ribas.

Ya ce irin wannan hali na rashin kunya da gwamnan ya nuna kaɗai ya isa a tsige shi daga kan madafun iko.

Cif Okocha ya ce:

“A matsayin jam’iyya, muna ba wa gwamna shawara: akwai zaɓi biyu kawai, ko dai ya yi murabus cikin mutunci ko kuma a tsige shi, wannan ita ce matsayar APC. Ba za mu tsaya muna kallo yana cin mutuncin shugaban ƙasa ba.
"Laifuffukan da ya aikata sun wuce a a ƙirga. Kotun Koli ta tabbatar da hakan har ma ta samar da ƙarin shaidu a kansa. Majalisar Dokoki ba ta bukatar kafa wani kwamitin bincike.
“Gaskiya sa’o’i 48 ma sun yi yawa a matsayin wa’adin da muka ba shi. Ya kamata kawai ya yi murabus cikin mutunci.”

Kara karanta wannan

Nasir El Rufa'i ya sauya sheka, ya fita daga APC zuwa SDP

Rikicin siyasar Ribas ya ƙara kamari

Wannan barazanar na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa tsakanin gwamnan da tsohon gwamna kuma ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ke ƙara kamari.

Tun bayan darewar Fubara kan mulki, dangantakar da ke tsakaninsa da magabatansa ta yi tsami, lamarin da ya haddasa rabuwar kawuna a Majalisar Dokokin jihar.

Wasu ‘yan majalisa sun tsaya tsayin daka domin kare gwamnan, yayin da wasu ke goyon bayan APC da Wike, rahoton Vanguard.

Okocha ya kara da cewa;

Ayyukan da gwamnan ke yi ba su da alaka da gaskiya ko adalci. Yanzu lokaci ya yi da ya kamata a dauki matakin da ya dace domin dawo da doka da oda a jihar.”

A yanzu haka, ana jiran matakin da Gwamna Fubara zai dauka dangane da wannan matsin lamba da APC ke yi masa.

Idan har ya gaza yin murabus kamar yadda aka bukata, akwai yiwuwar a fara shirye-shiryen tsige shi daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

Majalisa ta ba Gwamna Fubara kwanaki 2

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ribas ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa'adin kwanaki biyu ya sake ya miƙa sunayen kwamishinoni da ya naɗa.

Majalisar ta kuma zargi gwamnan da saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya ta hanyar yin nade-nade a ofisoshin da ke bukatar amincewar majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng