‘Sai Dai Trump Ya Mika Wuya’: Dan Majalisa a Iran game da Yaki da Amurka

‘Sai Dai Trump Ya Mika Wuya’: Dan Majalisa a Iran game da Yaki da Amurka

  • Wani dan majalisar Iran, Ebrahim Rezaei ya ce al'ummar Iran ba za su amince da mika wuya ba, yana mai cewa Amurka ce ya kamata ta mika wuya
  • Kakakin kwamitin tsaro na majalisar Iran ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump yana da zabuka biyu kacal, dukansu mika wuya ne
  • Rundunar sojin Iran ta ce za ta ci gaba da mayar da martani kan harin Amurka, tare da rufe mashigin Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Kakakin kwamitin tsaro da harkokin wajen majalisar Iran, Ebrahim Rezaei ya yi fatali da maganar mika wuya a yakin da ake yi da Isra'ila da kuma Amurka.

Rezaei ya tabbatar a ranar Alhamis 11 ga watan Yunin 2026 cewa al'ummar Iran ba za su taba amincewa da mika wuya ba.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai,an hallaka jami'an kasar Indiya

Dan majalisa ya bukaci Amurka ta mika wuya a yaki da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump, jagoran addini na Iran Mojtaba Khamnei Hoto: Donald J Trump/Imam Sayyid Mojtaba Khamnei.
Source: Getty Images

Rezaei ya bayyana haka da wani sako da ya wallafa a shafin X, wanda wakilin Legit Hausa ya samu a yau Alhamis 11 ga watan Yunin 2026.

Yadda Amurka ta kaddamar da sabon hari

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce sojojin Amurka sun kaddamar da wani sabon hari kan Iran da sanyin safiyar ranar Alhamis 11 ga watan Yunin 2026, lamarin da ya kara tsananta rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

A martanin da ta mayar, Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta rundunar sojin Iran ta sanar da cewa za ta ci gaba da mayar da martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar.

Rundunar ta kuma bayyana rufe mashigin Hormuz ga kowane irin jirgin ruwa, tana mai gargadin cewa za a kai hari kan duk wani zirga-zirgar ruwa da zai yi yunkurin bi ta wannan hanya.

Matakin ya kara nuna yadda rikicin ke kara kamari, yayin da duniya ke ci gaba da sanya ido kan yadda al'amuran za su kasance a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya aiko sako daga kasar waje bayan ba da umarnin kama shi

'Wanda ya kamata ya mika wuya a yaki'

Rezaei ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kasa mai tsayin daka wacce ba za ta kaucewa ra'ayin da take kai ba.

Dan majalisar ya jaddada cewa bangaren da ya kamata ya mika wuya a wannan rikici shi ne Amurka a yakin da ya ki ci ya ki cinyewa a Gabas ta Tsakiya.

Ya ce:

"Shugaban Amurka Donald Trump yana da zabuka biyu ne kawai, a cewarsa, ko dai ya mika wuya ko kuma ya mika wuya, yana nuni da matsayar Iran kan takaddamar da take yi da Washington."

Trump ya sake yi wa Iran barazana

Mun ba ku labarin cewa an yi ta musayar wuta tsakanin kasar Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya soki Iran kan abin da ya kira jan kafar da ta yi wajen tattaunawa domin cimma yarjejeniya.

Donald Trump ya nuna cewa Iran ta rasa damar da ta samu domin kulla yarjejeniya mai kyau, domin yanzu za ta dandana kudarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.