Bayan Cikar Wa'adi, Majalisar Dokoki Ta ba da Umarnin Kama Shugaban Hukumar Zabe

Bayan Cikar Wa'adi, Majalisar Dokoki Ta ba da Umarnin Kama Shugaban Hukumar Zabe

  • Yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ke kara tsananta a ƴan kwanakin nan, Majalisar dokoki ta sa kafar wando ɗaya da hukumar zaɓe watau RSIEC
  • A zamanta na yau Litinin, 10 ga watan Maris, Majalisar Dokokin Ribas ta ba da umarnin kamo shugaban hukumar zaɓe ta jiha, Adolphus Enebeli
  • Ta ɗauki wannan matakin ne bayan shugaban hukumar zaɓen tare da ƴan tawagarsa sun ƙi amsa gayyatar da majalisar da aika masu har wa'adi ya wuce

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Majalisar Dokokin Ribas, ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Martins Amaewhule, ta ba da umarnin kama shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (RSIEC).

Majalisa ta ba da wannan umarni na kama shugaban RSIEC, Adolphus Enebeli, sakamakon ƙin amsa gayyatar da ta yi masa domin ya bayyana gabanta.

Majalisar dokokin jihar Rivers.
Majalisa ta fusata, ta ba da umarnin kamo shugaban RSIEC Hoto: Martins Amaewhule
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a zamanta na ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin bada umarnin kama shugaban RSIEC

Majalisar ta ce Enebeli ya bijirewa umarnin da ta ba shi na bayyana a gabanta don ya yi bayani kan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar a ranar 5 ga Oktoba, 2024.

Hukumar RSIEC ta shirya gudanar da sabon zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 9 ga Agusta, 2025, bayan da Kotun Koli ta soke zaɓen da aka yi a shekarar da ta gabata.

Majalisar ta buƙaci shugaban RSIEC da kwamishinoninsa su bayyana domin su yi mata cikakken bayani kan dalilan da suka sa aka soke zaɓen da kuma shirin da ake yi na gudanar da sabon zaɓe.

Majalisa ta gayyaci shugaban hukumar zaɓe

Da farko, majalisar ta ba da wa’adin sa’o’i 48 domin Enebeli ya bayyana a gabanta, amma bai sa mu halarta ba, sai majalisar ta ƙara masa wa’adin zuwa sa’o’i 72.

Duk da haka, har yanzu bai bayyana ba, lamarin da ya sa majalisar ta ɗauki matakin ba da umarnin kama shi domin tilasta shi ya bayyana a gabanta, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

Shugabannin RSIEC sun kai ƙara kotu

A gefe guda, Enebeli da kwamishinonin hukumar sun shigar da ƙara a babbar kotun jihar Ribas, inda suka kalubalantar matakin da majalisar ta ɗauka.

Sun yi zargin cewa majalisar ba ta da hurumin tilasta masu su bayyana gabanta, kuma suna neman kotu ta dakatar da matakin da majalisar ke shirin ɗauka a kansu.

Yayin da majalisar ke matsa lamba kan ganin an gurfanar da shugaban RSIEC a gabanta, ana ganin wannan takaddama za ta ƙara dagula lamarin siyasa a jihar Ribas.

Majalisa ta dawo da shirin tsige gwamna

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fara yunkurin dawo da batun tsige Gwamna Siminalayi Fubara bayan ya ƙi bin umarninta kan kasafin 2025.

Hakan dai na zuwa ne bayan rigimar Majalisa da ɓangaren gwamnatin Fubara ta ɗauki sabon salo tun bayan hukuncin kotun ƙolin Najeriya wanda ake ganin ya warware rikicin Ribas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262