"PDP Ta Mutu Murus," Minista Ya Fadi Yadda Tinubu zai Yi Nasara a Zaben 2027

"PDP Ta Mutu Murus," Minista Ya Fadi Yadda Tinubu zai Yi Nasara a Zaben 2027

  • Ministan Harkokin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC, karkashin shugabancin Bola Tinubu, za ta ci zabe a 2027
  • Haka kuma, ya ce PDP za ta fadi a jihar Delta a zabukan nan gaba saboda rashin tasirinta a tsakanin al'umma da kuma irin tasirin APC a yanzu
  • Keyamo wanda babban lauya ne ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na APC da su hada kai domin tabbatar da cigaban jam'iyyar kafin zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta - Ministan harkokin jiragen sama da ci gaban sashen, Festus Keyamo, ya yi hasashen jam'iyyarsa ta APC, karkashin Bola Tinubu ce za ta koma mulkin kasar nan a 2027.

Ministan ya kuma bayyana cewa jam'iyyar PDP da ke mulki a Jihar Delta “za ta fadi” a zabukan nan gaba, saboda ta rasa tasirin da ta ke da shi a kasa baki daya.

Kara karanta wannan

2027: An gano manyan dalilai 2 da suka sanya El Rufai ya bar APC, ya koma SDP

Tinubu
Jagora a APC ya yi hasashen nasara a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa Festus Keyamo ya yi wannan furucin ne a Ughelli, Jihar Delta, yayin da yake maraba da Great Ogboru, dan takarar gwamnan Jihar Delta na jam'iyyar APGA a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Keyamo ya bayyana Ogboru a matsayin babban jagora da zai taimaka wajen ci gaban APC a jihar Delta, musamman a babban zabe mai zuwa.

Minista ya yabi tsohon dan takaran APC

Festus Keyamo ya kuma yabawa Ogboru kan yadda yake jagoranci cikin kwarewa, yana mai yaba yadda ya rike magoya bayansa ba tare da suna da gwamnati a hannu ba.

Keyamo ya bayyana cewa:

“PDP za ta fadi a Delta a zaben nan gaba. Shugaban kasa (Bola Tinubu) ya riga ya lashe zaben 2027.”
“An yi rashin nasara a Jihar Delta a 2023 ne kawai saboda wasu manyan masu ruwa da tsaki sun bar APC cikin fushi."

Keyamo ya nemi tallafin membobin APC

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

Keyamo ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki na APC a Jihar Delta da su ci gaba da goyon bayan jagorancin jam'iyyar don tabbatar da ci gaba da nasara a cikinta.

Tinubu
APC ta ce PDP ta mutu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Keyamo ya kara da cewa:

“APC ta kowa, ba jam'iyya ta mutum daya ba ce. Ba a da wani jagora guda daya a APC na Delta.”
“Muna da jagoranci na hadin kai. Kuma mun samu damar jagorancin shugaban kasa don ci gaba da hada kan jam'iyyar a Delta.”

"Karshen Jam'iyyar PDP ya zo" - Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa jam'iyyar PDP mai adawa shaguɓe a ranar Juma'a, ya ce ta na dab da mutuwa.

Abdullahi Ganduje ya zargi PDP da rikicin cikin gida da take fama da shi wanda ya ƙi ci ya ƙi cinye wa zai kawo wa jam'iyyar babbar matsalar da za ta kawo karshenta a nan kusa.

Kara karanta wannan

"An yi rashin nasara sau 3," Shugaba a PDP ya ja kunne kan tsaida Atiku takara a 2027

Shugaban jam'iyyar ya yi wannan magana ne yayin da yake karɓar wasu masu goyon bayan Atiku Abubakar waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng