2027: An Gano Manyan Dalilai 2 da Suka Sanya El Rufai Ya Bar APC, Ya Koma SDP

2027: An Gano Manyan Dalilai 2 da Suka Sanya El Rufai Ya Bar APC, Ya Koma SDP

Kaduna - Yanzu dai ta tabbata cewar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fice daga APC, ya koma SDP. Tambayar da kowa ke yi ita ce, me yasa ya yi haka?

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mallam Nasir El-Rufai yana daya daga cikin wadanda suka assasa kafuwar jam'iyyar APC a Najeriya, kuma ya taka rawa har ta ci zaben farko a 2015.

Me yasa zai bar ta yanzu?

El-Rufai ya bayyana dalilan da suka sanya ya sauka sheka daga APC zuwa SDP
El-Rufai ya zayyano wasu dalilai da suka sanya ya fice daga APC ya koma SDP. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP

A cikin wasikar da ya fitar a shafinsa na Facebook, El-Rufai ya sanar da komawarsa jam'iyyar SDP a hukumance, bayan barin APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya ce ba zai taba manta lokacin da suka yi gwagwarmayar hade kan jam'iyyun siyasa domin ganin an kafa hadaddiyar jami'yya ta APC ba.

Kara karanta wannan

'Mutuwa ce kawai za ta raba ni da APC,' Tarihi ya tuna maganganun El Rufa'i

"Burina tuna shekarar 2013 shi ne ganin cewa muraduna da na APC sun ci gaba da tafiya a kan turba daya har zuwa lokacin da na yanke shawarar ritaya daga siyasa."

- Nasir El-Rufai.

Sai dai, tsohon gwamnan ya ce a cikin 'yan shekaru biyun nan, ya tabbatar da cewa ba zai iya ci gaba da zama a inuwa daya da APC ba, saboda muradunsu sun sha bamban yanzu.

Dalilan da suka sa El-Rufai ya fice daga APC

Legit Hausa ta yi nazarin wasikar El-Rufai, tare da tattaro wasu dalilai da suka sanya tsohon gwamnan na Kaduna ya yanke shawarar watsar da APC.

1. Rikicin jam'iyyar APC

Dalilin farko da tsohon gwamnan ya bayar na ficewa daga APC shi ne rikicin cikin gida na jam'iyyar da shugabanninta suka kasa magancewa.

A cikin wasikarsa, El-rufai ya ce:

"Abubuwan da suka faruwa a shekaru biyun nan sun nuna cewa wadanda ke juya akalar APC, ba su da niyyar magance matsalar da jam'iyyar ke ciki."

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan Kaduna ya yi magana da El Rufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP

Tsohon gwamnan ya ce ya gabatar da korafe-korafensa ga shugabannin jam'iyyar amma babu wani sauyi, har ta kai ya fara fitowa a kafofin watsa labarai yana magana.

Rashin karewar rikice-rikicen jam'iyyar, da kuma kin daukar shawarwarinsa, ya sa El-Rufai ya ga cewar gwamnda ya nemi wata jam'iyyar kawai ya huta da matsalar APC.

2. "Jam'iyyar APC ta bar ni yanzu" - El-Rufai

Malam Nasir El-Rufai ya fice daga APC, ya koma SDP
Dalilan da suka sanya El-Rufai ya fice daga APC, ya koma SDP. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Ba tun yanzu ba, El-Rufai ya sha fadin cewa jam'iyyar APC ta mayar da shi saniyar ware a harkokinta, kamar dai ba da shi ne aka kafa ta, har ta ci zaben 2015 ba.

A wata hira da ya yi da Arise News a kwanakin baya, wadda Legit Hausa ta kawo, mun rahoto El-Rufai ya tabbatar da cewa ba shi ne ya bar APC ba, jam'iyyar ce ta barshi.

A wannan karon ma, daga cikin dalilansa na ficewa daga jam'iyyar, El-Rufai ya ce:

"Wadanda suka assasa wani abu, suna jin tamkar wannan abun ya zama jinin jikinsu, amma da zarar wannan abun ya sauya daga dalilin samar da shi, sai su fara neman mafita.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheka, El Rufa'i ya fadi yadda zai jawo rugujewar APC a Najeriya

"Na bautawa APC kuma na ba da gagarumar gudunmawa wajen kafuwarta, amma yanzu na fahimci jam'iyyar ta barni, ta barni kawai da tunanuka na ubannin da suka kafa ta."
"Duk kokarina na ganin nasarar APC a zabukan, 2025, 2019 da 2023 sun tashi a banza. Shekaru takwas da na yi a gwamnan Kaduna sun tafi wajen ci gaban jama'a, inganta kiwon lafiya, ilimi, samar da ayyukan yi, jawo masu zuba jari.
"Sai dai, duk da wannan tarin kokarin, jam'iyyar APC ta yanzu ta zabi wulakanta wadanda suka kafata, ta wancakalar da duk wani kokarinsu, a cikin shekarun nan biyu. Ba zan iya ci gaba da jure hakan ba."

Ya zuwa yanzu, jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan sauya shekar Malam Nasiru.

El-Rufai dai fitaccen dan siyasa ne a Arewacin Najeriya, kuma akwai masu ganin sauya shekarsa za ta yi tasiri ga jam'iyyar APC.

'Zan kalubalanci APC a 2027' - El-Rufai

Kara karanta wannan

"Mai jiran gado": Martanin 'yan Najeriya bayan El Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya jaddada aniyarsa ta kalubalantar APC a dukkanin zabukan shekarar 2027.

El-Rufai ya bayyana kudurinsa na zama ciwon ido ga tsohuwar jam'iyyar tasa ne a ranar Litinin, 10 ga Maris, a sanarwar sauya shekarsa zuwa SDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin, ta hanyar ba da shimfida ga tasirin El-Rufai a siyasar Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng