Keyamo Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Cikin Lauyoyin Da Za Su Kare Tinubu

Keyamo Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Cikin Lauyoyin Da Za Su Kare Tinubu

  • Festus Keyamo ya yi wa yan Najeriya bayani kan dalilin rashin kasancewarsa cikin jerin lauyoyin da za su wakilci Bola Tinubu a kotun zabe
  • Babban lauyan ya ce a matsayinsa na minista a gwamnati mai ci, doka bata bashi damar kasancewa cikin kowace tawaga ta lauyoyi ba
  • Keyamo ya ce zai iya shiga sahun lauyoyi masu kare Tinubu ne bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki

Babban lauyan Najeriya kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Festus Keyamo, ya yi bayani kan dalilin da yasa ba a ga sunansa a cikin tawagar lauyoyin da za su wakilci Bola Tinubu a kotu ba.

Za dai a shiga kotu tsakanin Tinubu da sauran yan takarar shugaban kasa kan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Festus Keyamo da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
Keyamo Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Cikin Lauyoyin Da Za Su Kare Tinubu Hoto: APC, Festus Keyamo
Asali: UGC

Minista mai ci ba zai iya tsayawa Tinubu ba sai bayan mika mulki, Keyamo

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 7 ga watan Maris, Keyamo ya ce ba zai iya kasancewa a jerin ba saboda kasancewarsa minista hakan zai saba kundin tsarin mulkin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A safiyar ranar Talata ne jerin sunayen lauyoyi 48 da za su wakilci Tinubu a kotu ya yi fice a soshiyal midiya. Sai dai kuma ba a ga sunan Keyamo a ciki ba.

Da yake kare kansa, Keyamo ya ce:

"Ga wadanda ke tambaya, minista mai ci (bisa kundin tsarin mulkinmu) ba zai iya kasance a tawagar lauyoyi masu zaman kansu ba, koda dai yana/tana iya taimakawa tawagar da shirye-shirye.
"Saboda haka, ministocin gwamnati mai ci wadanda suka kasance SAN za su iya shiga tawagar karar zabe ne bayan ranar 29 ga watan Mayu."

Kara karanta wannan

Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya

PDP ta zargi INEC da shirin goge shaidu a zaben shugaban kasa

A wani labari na daban, jam'iyyar PDP mai adawa a kasar ta zargi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da kokarin goge shaidun da ke tabbatar da an yi magudi a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairun 2023.

A cewar PDP, INEC na shirin yin hakan ne ta hanyar sake saita na'urorin BVAS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel