Wasu Tsoffin Ministocin Buhari Sun Taso Keyamo a Gaba Kan Binciken EFCC, Su Na Neman Ya Janye

Wasu Tsoffin Ministocin Buhari Sun Taso Keyamo a Gaba Kan Binciken EFCC, Su Na Neman Ya Janye

  • Wasu daga cikin tsoffin Ministocin Buhari sun yi ca kan Ministan jiragen sama, Festus Keyamo kan binciken EFCC
  • Ministan ta tabbatar da cewa hukumar EFCC ta fara bincike kan badakalar kwangiloli a ma’aikatar
  • Keyamo ya kasance tsohon Minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Da alamu Ministan Harkokin Jiragen Sama, Festus Keyamo zai shiga matsala kan bincikar badakalar kudade.

Keyamo ta tabbatar da cewa hukumar EFCC ta fara bincike kan badakalar kwangiloli a ma’aikatar.

An taso Ministan jiragen sama a gaba kan binciken EFCC
Minista Keyamo ya shiga matsala kan binciken EFCC. Hoto: Festus Keyamo.
Asali: Facebook

Wace matsala Keyamo ke ciki?

Sai dai da alamu hakan bai yi wa wasu tsoffin Minisocin Buhari dadi ba da ke ganin hakan zai jefa su cikin matsala, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Keyamo ya kasance tsohon Minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da su.

Kamar yadda wani daga cikin tsoffin Ministocin ya bayyana wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce wasu Minsitoci sun yi zama kan hakan.

Ya ce da yawa daga cikin tsoffin Ministocin su na ganin hakan bai dace ba ganin yadda shi ma Keyamo ya na daga cikinsu a gwamnatin da ta shude.

Martanin wani tsohon Minista

Ministan ya ce:

“Muna jin cewa Keyamo na daga cikin gwamnatin Muhammadu Buhari bai kamata ya sako tsohon Ministan a gaba ba.
“Dukkan tsoffin Ministocin su na cikin manhajar ‘WhatsApp’ inda suke mu’amala, sun kuma bukaci a yi wa Keyamo magana kan haka.”

Hakan bai rasa nasaba da tuhumar tsohon Ministan jiragen sama, Hadi Sirika da hukumar ta ke yi a kwanakin nan., Cewar Tori News.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shigar da sabbin tuhume-tuhume kan fitaccen malamin Musulunci a gaban kotu

Wani tsohon Minista ya tura sako a manhajar 'WhatsApp' ya na tambayar meyasa Keyamo zai yi haka.

Ya kara da cewa a shirye suke da tunkararsa kan haka bai kamata ya yi wanda suka yi aiki tare haka ba.

EFCC ta dakile biliyan 3 a hannun kanin Minista

Kun ji cewa hukumar EFCC ta bankado wata badakalar kwangilar naira biliyan takwas da ake zargin tsohon Ministan Buhari.

Ana zargin Hadi Sirika da bayar da kwangilar ga kaninsa mai sun Abubakar Ahmed Sirika har guda hudu.

Hukumar ta yi nasarar cafke Abubakar da kuma dakile naira biliyan uku daga cikin makudan kudaden.

Asali: Legit.ng

Online view pixel