Wata Sabuwa: Ganduje Ya Sa Lokacin Yin Jana'izar PDP, Ya Yi Gayyata
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa PDP mai adawa a Najeriya na dab da rugujewa
- Dr. Ganduje ya bayyana cewa PDP ta mutu murus saboda rikicin cikin gida da ya addabe ta, wanda yaƙi ci ya ƙi cinyewa
- Shugaban na APC ya nuna hakan ya fito a jihar Anambra inda jam'iyyar ta kasa samun ɗan takara a zaɓen gwamnan da ke tafe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa PDP mai adawa a Najeriya shaguɓe.
Abdullahi Ganduje ya yi wa PDP shaguɓen ne kan rikicin cikin gida da take fama da shi wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Asali: Facebook
Ganduje ya yi wannan magana ne a Abuja a ranar Juma’a, lokacin da ya karɓi wasu masu sauya sheƙa zuwa APC, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu sauya sheƙar dai wasu mambobin ƙungiyoyin goyon bayan Atiku Abubakar ne a zaɓen 2023, waɗanda suka koma jam’iyyar APC mai mulki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Me Ganduje ya ce kan halin PDP?
Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu murus, inda ya ba da misali da yadda ta kasa samun wanda zai yi takara a ƙarƙashinta a zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Shugaban na jam’iyyar APC ya ce babu ɗan takarar da ya nuna sha’awar yin takarar zaɓen gwamnan mai zuwa ne saboda rikicin da ya daɗe yana addabarta.
“Kun iso jam’iyyarmu. Yanzu muna karɓarku a hukumance. Amma kamar yadda aka sanar da ni, bayan lokacin azumi, duk mambobinku za su taru a nan Abuja, ƙarƙashin jagorancin Sanata Barau."
"Domin mu gayyaci shugaban ƙasa da mataimakinsa, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai, domin su karɓe ku a hukumance, tare da yin bikin binne PDP a Najeriya."

Kara karanta wannan
"Ɗan takara 1 tal gare mu," Sanatan APC ya hango wanda zai ci gaba da mulkin Najeriya a 2027
“Na ga wani bidiyo da ke yawo. Nan ba da daɗewa ba za a yi zaɓe a jihar Anambra. Kowace jam’iyya na shirin fitar da ƴan takararta domin yin takara a zaɓen gwamna."
“Amma na ga PDP ta tsawaita wa’adin tantance ƴan takararta saboda babu wanda ya bayyana don yin takara. Har wa’adin ya ƙare aka ƙara lokaci, amma babu wanda ya fito takara. Don haka, ba sai na faɗa ba, jam’iyyar na gab da rugujewa."
“Muna cin gajiyar rugujewar wannan jam’iyya. Saboda haka, muna maraba da ku da gaske. Muna maraba da ku zuwa jam’iyya mai kyakkyawan tsari."
“Zuwa jam’iyyar da ta yarda da bin doka. Zuwa jam’iyyar da ta yarda da dimokuraɗiyyar cikin gida. Zuwa jam’iyyar da ta yarda da haɗin kai. Zuwa jam’iyyar da ba ta yarda da nuna wariya ba."
- Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon ɗan majalisa ya bar PDP zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Edo, Nicholas Ossai, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Tsohon ɗan majalisar wanda ya wakilci Ndokwa ta Gabas/Ndokwa ta Yamma/Ukwuani ya bayyana cewa ya koma APC ne domin ya goyawa shugaba Bola Tinubu baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng