Minista Ya Fito da Karin Bayanan Dauke Hedikwatar FAAN Daga Abuja Zuwa Legas

Minista Ya Fito da Karin Bayanan Dauke Hedikwatar FAAN Daga Abuja Zuwa Legas

  • Festus Keyamo ya yi karin haske game da kudin da aka kashe a dalilin barin hedikwatar FAAN a Abuja
  • Ministan harkoki da cigaban jiragen ya ce an batar da alawus na DTA na kusan N500m a kan ma’aikata
  • Mai girma Ministan ya ce tafiye-tafiye daga Abuja zuwa Legas ya sa an kashe N1bn a cikin shekara guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan harkoki da cigaban jiragen sama, Festus Keyamo, ya cigaba da bayani a game da canza hedikwatar FAAN.

Festus Keyamo ya yi hira a gidan talabijin, inda ya yi bayanin hikimar sake dauke hedikwatar hukumar FAAN daga birnin Abuja.

FAAN.
FAAN: Ministan jiragen sama Hoto: @FKeyamo
Asali: Twitter

FAAN: Ana batar da kudi Abuja-Legas

Ministan jiragen saman ya nuna kudin da ake kashewa wajen zirga-zirgan manyan jami’an FAAN daga Abuja zuwa Legas ya yi yawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta saki bayanai, EFCC tana binciken fitaccen Minista a mulkin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya sai Festus Keyamo ya fito shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter, yake cewa yanzu ya samu karin bayani game da lamarin.

Ministan ya kara cewa kudin da aka kashe a shekarar bara wajen zarya ya kusa kai N1bn sa'ilin da gwamnati ke kukan karancin kudi.

A tsarin aiki, idan jami’ai sun yi tafiya daga ofishinsu zuwa wani wuri, gwamnati tana biyansu alawus musamman da ake kira DTA.

Hedikwatar ma'ikatu 7 za su koma Legas

Keyamo wanda ya dare kujerar Hadi Sirika, ya yi ikirarin babu isassun ofisoshi a Abuja, Premium Times ta kawo wannan rahoto.

A hirar da aka yi da ministan an fahimci ma’aikatu da hukumomi bakwai ake shirin dauke hedikwatarsu daga garin Abuja zuwa Legas.

Maganar Festus Keyamo a kan FAAN

“A lokacin da aka yi hira a tashar Channels da ni a jiya (Laraba), ba ayi mani bayanin kudin da hukumar FAAN ta kashe a shekarar bara kurum a kan DTA (alawus na tafiye-tafiyen) manyan ma’ikatan da ke yawo daga Legas zuwa Abuja kusan kullum ba,

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

Alawus na DTA ya kai N493m, baya ga kudin tikitin jirgin sama da aka kashe N451m.
Saboda haka gaba daya, saboda an hakikance a kan barin Abuja a matsayin hedikwatar FAAN (alhali babu ofisoshi a Abuja da za su dauki duka manyan jami’an), FAAN ta kashe kusan N1bn a shekara guda.”

- Festus Keyamo

Festus Keyamo a kan Nigeria Air

Ana da labari Festus Keyamo ya soki kwangilar Nigeria Air, ya ce abin ba komai ba ne illa jirgin Ethiopian Air ne dauke da tutar Najeriya.

Ministan ya shaida cewa EFCC tana binciken wannan kwangila kuma ana gudanar da binciken laifi a kan magabacinsa watau Hadi Sirika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel