Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Koma Jam'iyyar SDP don Ƙulla Sabon Ƙawance da El Rufai?
- Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya karyata rahotannin da ke cewa ya koma jam’iyyar SDP bayan barin PDP
- Jita-jitar komawarsa SDP ta biyo bayan ficewar Nasir El-Rufai daga APC, ake zargin za su tunkari zabukan 2027 a jam'iyya daya
- Sai dai mai tallafawa tsohon gwamnan kan labarai, ya shaida cewa Bafarawa bai shiga wata jam’iyya ba, kuma bai shirin yin hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya karyata rahotannin da ke cewa ya koma jam’iyyar SDP mai alamar doki.
Ya ce jita-jitar da ake yaɗawa ba ta da tushe kuma tana rikitar da al’umma, ya bukaci ‘yan jarida su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa su.

Asali: Twitter
Bafarawa ya karyata shiga jam'iyyar SDP
Jita-jitar cewa Bafarawa ya koma SDP na zuwa ne jim kadan bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga APC zuwa SDP, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya haifar da rade-radin cewa Bafarawa ya koma jam'iyyar SDP ne domin kulla ƙawance da El-Rufai gabanin zabukan 2027.
Sai dai a wani martanin gaggawa, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Dr. Abubakar Umar, ya karyata ikirarin, yana mai cewa Bafarawa bai shiga wata jam’iyya ba, kuma ba ya shirin yin hakan.
Yayin da yake zantawa da manema labarai, Dr. Umar ya ce:
“Babu wasu hujjoji da ke tabbatar da wadannan rahotanni. Alhaji Bafarawa bai shiga SDP ko wata jam’iyyar siyasa ba.
“Bai yi hira da wata jarida kan hakan ba, kuma bai tattauna da wata kungiya kan komawa wata jam’iyya ba."
Bafarawa ya gargadi kafofin watsa labarai
Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2007, ya kasance fitaccen dan siyasa a Arewa da ma Najeriya ba ki daya.
A baya, ya taba kasancewa a jam’iyyun daban-daban, amma ya ce a halin yanzu burinsa shi ne ci gaban rayuwarsa, ba wai fafutukar siyasa ba.
Tsohon gwamnan ya kuma soki yadda ake samun yaduwar labaran bogi, yana mai kira ga ‘yan jarida da su guji wallafa rahotanni marasa tushe.
“Abin takaici ne yadda wasu ke yada karya, musamman a lokaci irin wannan da kasa ke bukatar hadin kai da kyakkyawan sadarwa,”
- Inji Dr. Umar.
"Lokaci zai nuna" - Bafarawa kan komawa SDP

Asali: Twitter
Wasu na ganin shirun da Bafarawa ya yi kan al’amuran siyasa a ‘yan watannin da suka gabata, ya kara jawo wadannan rade-radin yanzu.
Yayin da harkokin siyasa a Najeriya ke daukar sabon salo, Bafarawa ya bukaci ‘yan kasa su mai da hankali kan abubuwan da za su kawo hadin kai da cigaba.
Da yake bayani a karshen maganarsa, Dakta Umar ya ce lokaci ne zai nuna ko Bafarawa zai sake dawowa siyasa ko kuma zai ci gaba da harkokinsa na yanzu.
A halin yanzu, karyatawarsa ta kawo karshen rade-radin cewa ya shiga SDP, sai dai masu lura da siyasa za su ci gaba da bibiyar matakansa gabanin zabukan da ke tafe.
Bafarawa ya sanar da ficewarsa daga PDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya tsahirta daga harkokin siyasa, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Attahiru Bafarawa ya ce ficewarsa daga PDP za ta ba shi damar bude sabon babi na rayuwarsa wanda ke cike da kokarin gina kai, da nisantawa daga siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng