Kwamishinonin El Rufa’i Sun Bayyana Gaskiyarsu Kan Zargin Karkatar da N1.37bn
- Tsofaffin kwamishinonin Kaduna sun musanta zargin da ake yi masu na karkatar da N1.37bn, tare da ikirarin ana kokarin bata masu suna
- Sun soki umarnin kotu da ya amince a kwato adadin kudin daga wani asusu, kuma sun bayyana fargabar cewa ana kokarin zaluntar wasu
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shigar da bukata a kotu don sahale mata ta kwato kudin da ta ce ta gano an karkatar da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, sun mayar da martani kan sabon umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yi.
A ranar 28 ga Fabrairu, Mai shari’a H. Buhari na Babbar Kotun Tarayya ya bayar da umarnin kwace Naira biliyan 1.37 na wucin gadi da ake zargin an karkatar zuwa wani asusun sirri.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana zargin an biya Naira biliyan 1.3 cikin asusun wani kamfani da ba a yi rijista da shi ba kan kwangilar aikin layin dogo na Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Za a yi wa wasu kwace,” Kwamishinonin El-Rufa’i
Channels TV ta wallafa cewa a martaninsu, tsofaffin kwamishinonin El-Rufa’i sun jaddada cewa babu wani dalili da zai sa a gudanar da shari’a a kan kwace wasu kudi da ba a karkatar ba.
Sun bayyana umarnin kotun a matsayin zalunci da kuma cin zarafi da nufin kwace kadarorin mallakar wasu mutane, da hana masu hannun jari daga kasashen waje shigo wa kasar nan.

Asali: UGC
A cikin sanarwar da suka fitar, sun ce:
“Da farko, muna so mu bayyana cewa aikin layin dogo na Kaduna wani bangare ne na samar da kayayyakin more rayuwa da gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta tsara domin inganta Kaduna ta zama jiha mai tafiya da zamani.
“An tsara aikin wanda Majalisar Zartarwa ta jihar ta amince da shi tun a watan Oktoban 2015. Kudin da za a yi amfani da su wajen aikin sun fito ne daga cikin bashin Duniya wanda ya kai Dala miliyan 350.”
Kwamishinonin El-Rufa’i sun karyata ICPC
A cikin sanarwar, tsofaffin kwamishinonin sun kalubalanci wadanda suka kira masu yada karya da jita-jita da su gabatar da takardun gaskiya don su musanta abin da suka fada.
Sanarwar ta ce:
“Duba da girman aikin, wanda kudinsa ya kai tsakanin dala miliyan 600 zuwa 700, dole ne mu nemi hadin gwiwa da kasashen waje don samun kudin aiwatar da shi."
“Saboda haka, mun fara da tallata aikin a shahararrun jaridu na cikin gida da na duniya, ciki har da mujallar The Economist.
“A karshe, wani kamfani daga kasar Indiya mai suna Skipper ya samu kwangilar aikin. Sun dauki nauyin samar da kudin aikin daga wani bankin India da yawansa ya kai 85% na kudin gaba daya, yayin da gwamnatin Jihar Kaduna za ta bayar da 15%.
Sanarwar ta amince da cewa tsohuwar gwamnati ta biya kamfanonin Skipper da GTA Naira miliyan 890 domin biyan kudin nazarin yiwuwar aiwatar da aikin.
Gwamnatin El-Rufa’i ta ba da kwangilar layin dogo
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa aikin bai ci gaba ba sakamakon kin amincewa da bayar da wasu kudi daga gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ce:
“Sai dai, tsohon ministan kudi ya ki amincewa da hakan, yana mai cewa bashin kasashen waje da ke kan Najeriya yana karuwa matuka, kuma idan aka bai wa Jihar Kaduna lamunin bashin, zai fuskanci zargin nuna son kai. Saboda wannan matsala, ba mu iya ci gaba da aikin ba.
An zargi jami'an gwamnatin El Rufa'i da almundahana
A wani labarin, mun ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bayar da umarnin kwato Naira biliyan 1.37 da ake zargin an karkatar daga baitul malin Gwamnatin Jihar Kaduna.
ICPC ta ce kudin, wani bangare ne na abin da aka ware domin aikin jirgin kasa na zamani, wanda ba a kai ga aiwatarwa ba a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya kara sashen da ke jaddada kalaman da ke cikin sanarwar da aka fitar.
Asali: Legit.ng