Matashi 'Dan Shekara 25 Ya Fadi Dalilan Angonce wa da 'Yar Shekaru 39
- Mustapha PK ya auri Anty Samira duk da bambancin shekaru tsakaninsu, yana mai cewa soyayya ce ta haɗa su, ba kwadayi ba
- Ma'auratan sun bayyana cewa soyayyarsu ta fara ne bayan sun hadu a makarantar da Anty Samira ta je koyon fasahar networking
- Mustapha ya bayyana cewa cewa kyautatawa da halayen kirki da Anty Samira ke da su ne suka ja hankalinsa gare ta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Matashin nan, Mustapha PK, mai shekaru 25, ya auri amaryarsa, Anty Samira, giwar mata mai shekaru 39, inda ya bayyana cewa akwai soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu.
Ya ce aurensa da Anty Samira, wanda ya ba hankalin jama'a sosai, ba bisa ƙwadayin kuɗi ko son zuciya aka yi ba, domin yana da abin hannunsa.

Asali: Facebook
A wata hira da sababbin ma’auratan suka yi da Tubless Media Concept, wacce aka wallafa a shafin YouTube, sun bayyana cewa soyayya tsantsa ce ke tsakaninsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka yi auren matashin da amaryarsa
A hirar Anty Samira da Oga PK — kamar yadda take kiransa — sun shaku da juna ne bayan ta je koyon harkar networking a makarantar su da ke Kano.
Mustapha PK ya ce:
“A koyaushe idan zan yi mu’amala da mutum, ba na fiye mu’amala da masu kula da mata fiye da kima.”
Anty Samira ta ce tun farkon haɗuwarsu ta lura da cewa Mustapha PK mutum ne mai addini, kuma baya kule-kulen mata barkatai, sannan yana girmama jama’a.
Matashin ya yaba da halayen amaryarsa
Mustapha PK ya bayyana cewa irin yawan kyautatawar da Anty Samira ke masa ya sa son ta ya shiga zuciyarsa sosai har ya fara son aurenta.

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa ba shi kaɗai ba, har ma da mutanen gidansu suna yaba da kyautatawar Anty Samira da kyakkyawar mu’amalarta.
A nata ɓangaren, Anty Samira ta ce a lokacin da Mustapha PK ya bayyana mata sirrin zuciyarsa cike da so da kauna, ta so ta ƙi amincewa a farko.
Ta ce:
“Shi soyayya, mace za ta iya ba namiji idan ta so.”
Ta ƙara da cewa son Mustapha PK ya mamaye zuciyarta, kuma za ta ci gaba da yi masa biyayya a matsayinsa na mijinta, wanda ya wajaba ta yi masa biyayya.
Anty Samira Giwar mata, ta kara da shan alwashin cewa Mustapha PK zai samu kulawar da ba zai samu a wajen budurwa yar shekara 16-17 ba.
Rarara ya angonce da amaryarsa
A baya, mun kawo labarin cewa fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya angwance da Aisha Humaira a wani daurin aure da aka gudanar a jihar Borno.
An daura auren ne a ranar Juma’a, 25 ga Afrilu, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce musamman daga masu bibiyar harkokin fina-finai da siyasa, ganin cewa ba a yi sanarwa ba.
Dauda Kahutu Rarara ya bayyana murna da jin daɗinsa bayan da aka daura auren, inda ya bayyana A'isha Humaira a matsayin tantabara uwar alkawari, kuma abin alfaharinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng