Rahama Sadau Ta Tabo Maganar Aure, Ta Fadi Irin Bikin da Take so

Rahama Sadau Ta Tabo Maganar Aure, Ta Fadi Irin Bikin da Take so

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta bayyana sha’awarta ga bikin jaruma Priscilla Ojo da fitaccen mawakin Tanzaniya, Juma Jux
  • Sadau ta bayyana bikin a matsayin mai ban sha’awa, cike da abubuwan burgewa, kyau da kuma tsari mai kayatarwa tun daga farko har ƙarshensa
  • Bikin ya ja hankalin mutane a kafafen sada zumunta, inda aka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan bukukuwan da aka yi a 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bikin auren jarumar Nollywood Priscilla Ojo da mawakin Tanzaniya, Juma Mkambala wanda aka fi sani da Juma Jux, ya ɗauki hankali a kafafen sada zumunta.

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana jin daɗinta da yadda aka gudanar da bikin.

Rahama
Rahama Sadau ta yaba da yadda aka gudanar da bikin Juma Jux. Hoto: Rahama Sadau
Asali: UGC

Rahama ta wallafa a X cewa tana fatan samun biki irin na su yayin da ta yi kalmomin yabo da ke cike da sha’awa, tana cewa “Dukkan kayan da amarya ta saka sun kayatar.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Irin bikin da Rahama Sadau ke so

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa bikin Juma Jux ya kasance cike da salo mai ban sha'awa da ƙayatarwa, inda ta ƙara da cewa:

“Kowane ɓangare na bikin yana da kayatarwa. Amarya da abokanta sun yi kyau, sun yi kwalliya cikin kamala.”

Rahama Sadau ta bayyana cewa tana son irin bikin saboda yadda ya kayatar sosai kuma ba a samu wata matsala ba a cikinsa.

An yi bikin ne a ranar Asabar da ta gabata a birnin Lagos, inda manyan mutane da mashahuran mawaka suka halarta.

Rahoton Punch ya nuna cewa cikin wadanda suka halarci bikin akwai 'ya'yan mawaka kamar Imade, 'yar Davido da Liam, ɗan marigayi Mohbad.

Imade da Liam sun dauki hankalin jama’a

A wajen bikin, Imade ta taka rawar gani a matsayin ɗaya daga cikin yaran amarya, yayin da Liam ya zama mai ɗauko zobe.

Rahotanni sun nuna cewa lamari ya burge jama’a sosai, inda suka jinjina da ƙara nuna ƙauna ga ma’auratan.

Davido
Wasu 'yayan mawaka da suka halarci bikin. Hoto: @priscilla_ojo
Asali: Twitter

A makon da ya gabata kafin bikin, Priscilla da Juma sun fitar da hotunan kafin daurin aure guda biyar da suka girgiza intanet.

An ruwaito cewa ma'auratan sun saki hotunan suna bayyana soyayyarsu da kalmomi masu daɗi da cewa:

“Zukata biyu sun dawo ɗaya, tafiya ce ta har abada.”

Rahama Sadau da sauran mutane sun yaba da irin yadda aka tsara bikin daga farko har ƙarshe cikin nitsuwa.

Mahaifiyar Priscilla, Iyabo Ojo ta bayyana cewa ana shirin gudanar da babban bikin ƙarshe a Tanzaniya a watan Mayu.

Duk da haka, an samu wasu mutane kamar VDM da suka soki yadda bikin ya gudana a X, yana cewa amaryar ta yi karama ta yi aure tana shekaru 24.

Rahama Sadau ta yabi Sanusi II da suka hadu

A wani rahoton, kun ji cewa jarumar Kannywood ta bayyana cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II yana burge ta.

Legit ta wallafa cewa Rahama Sadau ta yi magana ne yayin da suka hadu da Muhammadu Sanusi II a filin jirgin sama.

Rahama Sadau ta bayyana cewa sun hadu ne ba tare da sanin cewa za su hadu ba, amma shigar sarkin na cikin abubuwan da yake burgeta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng