Turji Ya Zafafa Hare Hare a Sakkwato, Mazauna Kauyuka 20 Sun Fara Kaura

Turji Ya Zafafa Hare Hare a Sakkwato, Mazauna Kauyuka 20 Sun Fara Kaura

  • Mazauna wasu kauyuka da ke yankin Sabon Birni a jihar Sakkwato sun shiga uku saboda yawaitar hare-hare daga yaran Bello Turji
  • Wannan lamari ya jefa al’umma a cikin firgici, kuma ya nuna karara cewa barazanar da Turji da mabiyansa ke yi ba ta lafa ba
  • Sakamakon tsananin hare-haren da ake fama da su, mazauna akalla kauyuka 20 sun bar muhallansu domin tsira da rayukansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Sabon harin da ake zargin mutanen fitaccen 'dan bindiga, Bello Turji, ne suka kai, ya tayar da hankula a wasu daga cikin kauyukan jihar Sakkwato.

Wadannan jerin hare-hare da ake kai wa jama'a babu kakkutawa sun tilasta wa mazauna akalla kauyuka 20 barin muhallansu a jihar Sakkwato domin tsira da rayuka.

Sakkwato
Harin mayakan Turji sun raba jama'a da gidajensu Hoto: @ahmedaliyusok/@ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Wani bidiyo da wani mai suna Bakatsine ya wallafa a shafinsa na X ya nuna yadda waɗanda suka rasa matsuguni ke neman mafaka a Gatawa, wani gari da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin Bello Turji ya kori mazauna Sakkwato

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wani mazaunin yankin mai suna Mallam Saminu ya tabbatar da cewa yanzu jama'a suna barin gidajensu.

Ya bayyana cewa ƙauracewa garuruwan ya biyo bayan sababbin barazana da hare-hare da wani babban kwamandan Turji ke kai masu.

Ya ce:

"Eh gaskiya ne. Mutane daga kauyuka da dama da ke kewaye da Gatawa sun kauracewa garuruwansu sun zo nan neman mafaka.
"Wasu suna zama da ‘yan uwa a cikin gari, wasu kuma gwamnati ta basu mafaka a makarantu biyu – ɗaya yana kusa da sansanin soja, ɗaya kuma a cikin gari."

Kauyukan Sakkwato da jama’a suka bari

Kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Makira, Shabanza, Katsalle, Dan Kura, Garin Tunkiya, Dama, Dan Tazako I, II da III, Gaugai da sauran su da dama.

Gwamna
Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu Hoto: @ahmedaliyusok
Asali: Facebook

Har yanzu babu wani jami’i daga gwamnatin jihar Sakkwato da ya yi tsokaci a hukumance kan lamarin, musamman mashawarcin gwamna kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya).

A nasa bangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufai, ya ce zai yi bayani bayan ya samu cikakken rahoto kan halin da ake ciki.

Gudun hijira da wasu mazauna Sakkwato ke yi a halin yanzu ya kara tabbatar da mummunan halin rashin tsaro da sassan Arewa maso Yamma ke fuskanta.

'Mayakan Turji sun hana jama'a sakat,' Mazaunin Sakkwato

Kwamred OC Sakaba daga karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato ya shaidawa Legit cewa garuruwa na ci gaba da watsewa a yankin Gatawa.

Ya ce:

“Mun yi tunanin wannan fadan da ake yi zai dore, sai gashi mun ji cewa an daina. Wannan yasa barayin suka dauki matakin shiga kauyuka suna cin karensu babu babbaka, suna aikata wulakanci kala-kala.”

“Yanzu haka, garuruwa da dama sun watse, inda dubban mutane ke kwarara zuwa Gatawa domin neman mafaka.”
“Muna kira ga masu alhakin kare rayukan al’umma su ji tsoron Allah, su dauki kwararan mataki. Al’umma na cikin wani hali na ban tausayi.”

Yan bindiga sun kai hari Sakkwato

A baya, kun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 11 a wasu hare-hare da suka kai a ƙauyuka uku da ke cikin ƙananan hukumomin Gwadabawa da Sabon Birni a jihar Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigan sun far wa al’ummar yankin ne a daren Juma’a, 2 ga watan Mayu 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, suka bude wuta ba tare da kakkautawa ba.

Majiyoyi daga bangaren tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga masu tarin yawa da suka zo a kan babura sun fara farmakin ne a ƙauyen Satiru da ke karamar hukumar Gwadabawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.