'Alo Tsiya, Alo Danja,' Abdullahi Abbas Ya Ce APC za Ta Kwaci Mulkin Jihar Kano

'Alo Tsiya, Alo Danja,' Abdullahi Abbas Ya Ce APC za Ta Kwaci Mulkin Jihar Kano

  • Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya sake yin kalaman tada kura game da zabe, yana zargin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cutar da jama'a
  • A cikin wani bidiyo, Abbas ya ce dole APC ta lashe zabe, ko da ana alo tsiya, yana mai cewa ba za su yarda Kwankwasiyya ta sake yin nasara a 2027 ba
  • Wasu 'yan Najeriya sun bayyana damuwa kan kalamansa, suna zarginsa da amfani da harshe mai kaushi da ka iya tayar da hankula a gabanin zaben

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya sake maimaita wasu kalamai da suka jawo ce-ce-ku-ce dangane da harkokin siyasa.

A wani taron magoya baya, Abbas ya zargi gwamnatin jihar Kano da yi wa jama’a aika aika, da jefa su a cikin mawuyacin hali bayan an zabe ta.

Kwankwaso
Abdullahi Abbas ya ce APC za ta kwace mulki daga yan Kwankwasiyya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Abdullahi Abbas
Asali: Facebook

A cikin wani bidiyo da hadimin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya wallafa a shafinsa na Facebook, an jiyo Abbas yana cewa gwamnatin Kano ta cuci jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, akwai zarge-zarge na rushe gine-gine da wasu ayyuka da suka kara wa jama’a radadi, yana mai cewa saboda haka ne dole APC ta dawo mulki a zabe mai zuwa.

APC ta aika sako ga Kwankwaso

A cikin bidiyon, Abdullahi Abbas ya zargi gwamnatin Kano da satar kayan jama’a, baya ga rusau da ya ce ya jawo wa jama'a kuncin rayuwa.

Ya ce:

“An zo an ci mu da mari, an cuci mutane, an sace kudin mutane, an yaudari mutane. To muna gayawa Rabi’u Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya: Wallahi wannan zaben, duk abin da zai faru a Kano, ya faru.”

“Ana alo tsiya za a yi zabe” – Shugaban APC

Abdullahi Abbas ya sake amfani da kalamai masu zafi dangane da zaben da ke tafe a jihar Kano, yana mai cewa dole APC ta lashe zaben.

Abbas
Shugaban APC ya zargi gwamnatin Kano da yaudarar jama'a Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya ce:

“Za a yi zabe ana alo tsiya, alo danja, sai mun ci zabe ko ana so ko ba a so. A Kano a wannan zaben da za mu yi, ko da tsiya, ko da tsiya-tsiya.”
“Ina tabbatar muku, a cikin birni da kananan hukumomi, za a yi zabe ana alo tsiya, alo danja. Sai mun ci zabe ko ana so ko ba a so. Ba za mu yarda da wannan iskancin da aka yi ba.”

Jama’a sun soki kalaman shugaban APC

Wasu daga cikin masu amfani da Facebook sun bayyana rashin jin daɗinsu kan irin kalaman da shugaban APC ke furtawa, suna masu cewa hakan na iya tunzura jama’a.

Umar Usman Danlarabawa ya rubuta cewa:

“Wannan tsiya da kuke kira, Ubangiji ya haɗaku da ita.”

Kamilu Anadariya ya ce:

“Faduwar zabe ta haukata mutanen nan wallahi. Kuma ko mazabarsa ba zai iya lashe wa ba har abada.”

Abba Magaji Rijiya Biyu ya rubuta cewa:

“Ubangiji ya hanaku mulki, tunda duk abin da ba a nema ta hanyar halal ba, ƙarshe ba zai zama alheri ba.”

Minista ya fadi sharin APC na karbar Kwankwaso

A baya, mun wallafa cewa wasu jiga-jigan APC sun bayyana matsayinsu dangane da rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa cikinsu.

Daga cikin wadanda suka yi wannan martani har da ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, wanda ya ce basu da niyyar gayyatar Kwankwaso zuwa APC.

Karamin Ministan ya kara da cewa idan har shugaban jam'iyya, Abdullahi Ganduje bai amince da sauya shekar ba, to Rabiu Kwankwaso zai ci gaba da zama mutumin da ba sa muradi a APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.