Bayanin Rarara da Aisha Humaira bayan Daura Musu Aure a Maiduguri

Bayanin Rarara da Aisha Humaira bayan Daura Musu Aure a Maiduguri

  • An daura auren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara da fitacciyar jaruma, Aisha Humaira a Maiduguri a ranar Juma’a ba tare da sanar da jama’a ba
  • Rarara da amaryarsa sun bayyana farin cikinsu, inda suka bukaci a yi musu addu’a tare da fatan alheri ga duk wanda suka taba yi wa kuskure
  • Sanata Barau Jibrin ya halarci daurin auren, kuma ya bayyana cewa aure ne na soyayya tare da yin fatan zaman lafiya mai dorewa ga ma'auratan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - A cikin wani daurin aure da ya zo ba tare da wani shiri na jama’a ba, fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya angwance da Aisha Humaira.

An daura auren nasu ne a ranar Juma’a, 25 ga Afrilu, a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rarara
Rarara ya yi bayani bayan daura masa aure da Aisha Humaira. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

Dauda Kahutu Rarara ya bayyana farin cikin shi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurin auren ya ja hankalin mutane da dama musamman ma'abota fina-finai da siyasa, duba da cewa babu sanarwa ko taron jama’a kafin bikin.

Sai dai daga bisani, ma’auratan sun yi magana da manema labarai inda suka bayyana dalilin da yasa aka daura auren ba tare da sanarwa ba.

Dauda Kahutu Rarara ya bayyana farin cikinsa

Da yake bayani bayan daurin auren, Rarara ya bayyana cewa ya shiga rana mafi farin ciki a rayuwarsa.

Ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:

"Tattabara ’yar alkawari. Alhamdulillah yau rana ce ta farin ciki a wajena wanda ba zan taba mantawa da ita ba. Ina alfahari dake amaryata."

A cikin wata hira da ya yi da DCL Hausa, Rarara ya yi addu’ar fatan alheri ga duk wadanda suka samu halartar daurin auren, yana mai fatan kowa ya koma gida lafiya.

Da aka tambaye shi ko zai yi waka dangane da auren, ya ce kamar yadda ba a sanar da auren ba, hakanan idan akwai waka, daga baya za a ji.

Aisha Humaira ta roki afuwa da addu’a

Ita ma Aisha Humaira ta bayyana cewa an daura auren ba tare da wata sanarwa ba saboda an je saka rana ne kawai sai aka zabi a daura auren.

Bayan bayanin da Aisha Humaira ta yi, ta roki jama’a da su yi hakuri da kuma fatan alheri a kan auren da ta yi.

Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa:

"A yi hakuri, a yi mana fatan alheri. Da fatan duk wanda na taba yi wa kuskure zai yafe mani.
Ni ma duk wanda ya taba min wani abu – da wanda na sani da wanda ban sani ba – na yafe musu duniya da lahira."

Sanata Barau Jibrin ya halarci auren Rarara

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, yana cikin manyan bakin da suka halarci bikin.

Barau
Sanata Barau da Aminu Bello Masari a wajen daurin auren Rararara a Maiduguri. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Barau ya bayyana auren a matsayin wanda aka kafa bisa soyayya da niyyar zaman lafiya, inda ya ce:

"Muna taya su murna, muna kuma fatan a yi zaman lafiya. Muna fatan shekara mai zuwa za a gayyace mu suna."

Rahama Sadau ta fara maganar aure

A wani rahoton, kun ji cewa jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta fara hararo dakin miji bayan wani gagarumin biki da aka daura a Legas.

An daura auren wani mawaki ne mai suna Juma Juz dan asalin kasar Tanzaniya da matarsa 'yar Najeriya.

Rahama Sadau ta yaba da yadda aka gudanar da auren cikin ado da kayatarwa inda ta ce tana son a yi irin bikin a ranar aurenta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng