Takaitaccen tarihin bakin Attajirin Duniya Aliko Dangote

Takaitaccen tarihin bakin Attajirin Duniya Aliko Dangote

A yau ne Aliko Dangote yake bikin murnar cika shekaru 62 da haihuwa a Duniya. Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin wannan hamshakin dan kasuwa da duk Afrika babu kamar sa a yau.

Takaitaccen tarihin bakin Attajirin Duniya Aliko Dangote
Aliko Dangote yana cikin manyan masu kudi a Duniya
Asali: UGC

1. Haihuwa

An haifi Aliko Dangote ne a Afrilun 1957 a cikin Garin Kano. Mahaifin sa Muhammad Dangote, babban ‘dan kasuwa ne kuma ‘dan siyasa a lokacin jamhuriya ta farko wanda ya rasu tun Dangote yana karami.

Mahaifiyar sa Mariya Jika ce a gidan Alhasawa watau dangin Alhassan Dantata, wanda har yau tana raye.

2. Karatu

Aliko Dangote yayi karatun addinin Musulunci da kuma Boko a Kano, har ya zarce zuwa babbar jami’ar nan ta Al Azhar da ke kasar Masar inda ya karanta ilmin kasuwanci ya kuma kare yana shekara 21.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

3. Kasuwanci

Aliko Dangoye ya samu jarin da ya fara kasuwanci ne daga hannun Baffan sa a 1977. Tun kafi wannan lokaci, Aliko Dangote ya nuna sha’awar sa ta harkar kasuwanci da ya gada daga dangin Mahaifiyar sa.

Daga baya abubuwa sun budawa Aliko Dangote inda yayi kaimi a lokacin mulkin Obasanjo ta hanyar wani na-kusa da shi. Dangote ya rika jigilar kasuwanci zuwa kasashen waje tun kafin rasuwar Kakan sa.

4. Kamfanin Dangote

Daga baya Dangote ya bude kamfanin sa da ya radawa sunansa, bayan ya gawurta. Aliko Dangote ya daina harkar dillanci a 2005, inda ya koma hada taliya, fukawa, sukari, gishiri da siminti na kan sa ba tare da sayo na waje ya saida ba.

5. Dukiya

Yanzu dai Dangote yayi kaimi a kaf Duniya inda ya zama bakin mutumin da ya fi kowa arziki. Forbes tace Dangote ya ba fiye da fam Dala 10 baya kuma yana cikin manyan Attajiran Duniya a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng